• About Us
  • Blog
  • Gwamnatin Jihar Kano ta ce ana gabda fara ginin masana’antun Iskar Gas a Jihar
  • Home
Monday, March 20, 2023
  • Login
Dimokuradiyya
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Rahotanni
  • Wasanni
  • Rikicin Duniya
  • Nishadi
  • More
    • Kasashen Ketare
    • Kiwon Lafiya
    • Ilimi
    • Kasuwanci
    • Noma Da Kiwo
    • Labarun Mako
    • Talla
    • Masarautu
    • Babu Maraya
    • Addini
      • Wa’azin Kirista
    • Girke-Girke
    • Waiwaye
    • Marubutanmu
    • Wasiku
    • Ni’ima Dai Mata
    • Tsaro
    • Bidiyo
    • Audio
No Result
View All Result
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Rahotanni
  • Wasanni
  • Rikicin Duniya
  • Nishadi
  • More
    • Kasashen Ketare
    • Kiwon Lafiya
    • Ilimi
    • Kasuwanci
    • Noma Da Kiwo
    • Labarun Mako
    • Talla
    • Masarautu
    • Babu Maraya
    • Addini
      • Wa’azin Kirista
    • Girke-Girke
    • Waiwaye
    • Marubutanmu
    • Wasiku
    • Ni’ima Dai Mata
    • Tsaro
    • Bidiyo
    • Audio
No Result
View All Result
Dimokuradiyya
No Result
View All Result
Home Uncategorized

A Gaggauta Sanya Dokar Ta Baci A Fannin Ilimin Jihar Bauchi Don Farfado Da Shi -Ancopss

Mustapha Haruna Dabai by Mustapha Haruna Dabai
June 1, 2019
in Uncategorized
Reading Time: 4 mins read
1 0
0
2
SHARES
14
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Daga Uzairu Dauda, Bauchi

An bukaci sabon gwamnan jahar Bauchi sanata Bala Abdulkadir Muhammad, daya sanya dokar ta baci a bangaren ilimin sakandare domin samun kyakkyawan sakamako.

Shugaban kungiyar shugabannin sakandare ta Najeriya ANCOPSS reshen jahar Bauchi, Dr Musa Mudi Jahun, shi ya bayyana haka da yake jawabi wa manaema labarai a ofishinsa.

Yace ya kamata sabon gwamna ya soke takunkumin da aka sanyawa malamai na rashin Karin girma zuwa mataki na goma sha shida.

“Malamai ada, ana musu Karin girma daga matakin na goma 15 zuwa na 16 sai haka kawai aka soke bamusan dalili ba, amma har yanzu wasu jahohi da sukayi koyi damu har yanzu sunanan sunayi.

“Har yanzu a soke tsarin nan wanda akayi na cutar malamai, wanda kwata kwata malaman da suke mataki na sha shida a jahar Bauchi basu wuce 113 ba, sannan in mutum yayi ritaya a matakin albashi na 16 shida sai ace za a biyashi hakkinsa a matakin albashi na 15, wannan cin zali ne, keta ce wadda akayiwa malamai.

Muna rokon mai girma sabon gwamna daya soke wannan tsari, ya kamata duk matakin da mutum yayi ritaya a biyashi hakkinsa, babu yadda za ayi malami ya shafe shekara Talatin da biyar yana gwagwarmaya da kokari na cigaban ilimi har yaje mataki na sha shida da akace an soke kuma azo a biyashi hakkinsa a mtakin na sha biyar”.

Dr Mudi Jahun, sai ya bukaci gwamnan, daya bullo da tsari wanda zaina rike malamai a fannin koyarwa batare da sun gudu daga fannin ba zuwa wani fanni.

“Muna da kwararrun malamai wadanda suke da karatu masu zurfi, amma saboda babu tsarin da zai taimaki malamai yasa musu azama da karfafa gwiwa, suna ta barin sakandare suna komawa manyan makarantu. Muna da malamai dubu shida da dari uku da arba’in da takwas a karkashin ma’aikatar ilimi wadanda suka rage a yanzu basu wuce dubu hudu ba, duk sun watse sun tafi, muna da makarantu kimanin dari biyu da tara, amma ko ina kaje ba malamai, saboda haka gwamnati ta dawo da tsarin biyan alawus din da har yasa wasu malaman da suka gudu suke ta dawowa daga wasu ma’aikatu, dafatan mai girma gwamna zai duba wannan tsari na rike malamai a muhallinsu.

“Sannan muna rokon gwamna daya bincika yasa a biya shugabannin makarantu kudaden gudanar da jarabawa, a tarihin jahar Bauchi ba a taba samun lokacin da ba a biya malamai kudin jarabawa ba kamar a wannan lokaci. Abin takaici shine shugabnnin makarantun sakandare sun karbi basussuka a bankuna wasu kuma sun sayar da kadarorinsu ne don biyan kudin gudanar da jarabawar WAEC wasu kuma sun ari kudin NECO ne kuma har yanzu gwamnati bata biyasu ba, sannan ga jarabawar NECO na karatowa don haka suna cikin halin ni ‘yasu, wanda in ba a maida hankaliba wasu shugabannin sai an kamasu.

Comrade Musa Jahun, yayi nuni da yadda harkar ciyarwa a makarantun sakandare na kwana ta tababbare a halin yanzu da cewa, “ akwai shugabannin sakandaren da suka debe duk dukiyarsu suka ciyar da dalibai amma har yanzu gwamnati bata biyasu ba, akwai shugaban da yake bin naira miliyan uku, suna bin kudi kimamin naira miliyan tamanin na kudin ciyarwa a makarantu talatin da takwas da ake dasu a jahar Bauchi, saboda haka munaso mai girma gwamna ya bincika ya biyasu hakkokinsu, in ba haka zasu shiga wani hali da bazai hafar da da mai ido ba.

“ya kamata mai girma gwamna ya fito ko yazo mana da irin tsarin da yayi a makarantun birnin tarayya Abuja lokacin da yake ministan birnin tarayya wajen kyautata abincin makaranta, makwanni biyu da suka gabata munje taro a Abuja na ANCOPSS a GSS Gwagwalada, abin dadi shugabanmu na kasa ya zaga damu cikin makarantar muka shiga dakin ajiye abincinsu, sai aka tambayi shugaban GSS Gwagwalada kan irin sirrin da sukebi na ciyarwa suke samun nasara? Abin da shugaban makarantar ya fada shine, lokacin da sanata Bala yake ministan Abuja shine ya fito da wannan tsarin. Sai shugaban ANCOPSS na kasa ya juya ya cemun shugaban ANCOPSS na Bauchi muna tayaku murna, na tabbatar zakuyi irin wannan tsari baza ku samu matasala a Bauchi ba”.

Shugaban kungiyar ANCOPSS, ya yabawa yunkurin gwamnan na alkawarin hada gwiwa da hukumar NTI don horas da malamai akai akai, wanda yace sau daya aka tabayin hakan a gwamnatin data shude, sai yayi fatan wannan matakai zai dore idan an fara a wannan sabuwar gwamnatin Bala Abdulkadir.

Dr Jahun, yace batun inganta ilimi na fasaha da kere kere a jahar Bauchi da gwamnan yayi alkawari, yace jahar Allah ya albarkaceta da kwararrun malamai a wannan fanni cikin makarantun sakandaren kimiya da fasaha, abin da ya rage shine goyon baya da kudaden gudanar da amfani dasu.

Dr Musa Jahun ya bayyana cewa, ilimi a jahar Bauchi bai taba shiga ni ‘yasu da halin kakani kayi ba kamar cikin sheakarar karshe na gwamnatin tsohon gwamna Mohammed Abdullahi Abubakar.

Idan za a iya tunawa dai cikin shekara ta 2017 da 2018, jahar Bauchi ta samu cigaba a fannin jarabawar WAEC daga kashi 17.5 cikin dari zuwa kashi 26.7% na cin jarabawar karkashin tsohon gwamna Abubakar, cewar gwamnatin jahar.

Daga nan sai yayi alkawarin mara bayan kungiyar ANCOPSS dari bisa dari don gyaran ilimi a jahar Bauchi, tare da rokon gwmna Bala Abdulkadir Muhammad daya duba dukkan matsalolin da aka zayyana don daukar matakan dawo da hayyacin ilimi a jahar ta Bauchi.

Previous Post

Kasar Angola Ta Amince A Sake Yin Jana’izar Jonas Savimbi, A Karo Na Biyu

Next Post

Dan Shekara 38 Ya Zama Shugaban Kasar Salvador

Next Post

Dan Shekara 38 Ya Zama Shugaban Kasar Salvador

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result
Arabic Arabic English English French French Hausa Hausa
  • Ya ce mun shi Dillalin Motoci ne, bayan mun yi aure na gane Makanike ne

    Ya ce mun shi Dillalin Motoci ne, bayan mun yi aure na gane Makanike ne

    2455 shares
    Share 982 Tweet 614
  • Da Ɗumi-Ɗuminsa: Ƙazamin Rikici Ya Kaure Tsakanin Shugaban Ƙungiyar CAN Da Isa Ashiru Kudan

    1995 shares
    Share 798 Tweet 499
  • Sai na yi lalata da kai na kwanaki 4 babu ƙaƙƙautawa sannan zan taimaka maka, Wata mata ga saurayi

    1693 shares
    Share 677 Tweet 423
  • Ga Irinta Nan: Budurwa Ta Koka Bayan Saurayinta Ya Ƙi Amsar Cikin Da Ya Ɗirka Mata

    1365 shares
    Share 546 Tweet 341
  • CBN Ya Sake Fitar Da Sabbin Bayani Kan Dawo Da Tsofaffin Takardun Kudin Naira

    1592 shares
    Share 637 Tweet 398
Dan takarar LP Ya Taya Zababben Gwamnan Filato Murnar Lashe Zabe

Dan takarar LP Ya Taya Zababben Gwamnan Filato Murnar Lashe Zabe

March 20, 2023
An bai wa hammata iska tsakanin Sojoji da Yan sanda, Jami’ai biyu sun mutu

An bai wa hammata iska tsakanin Sojoji da Yan sanda, Jami’ai biyu sun mutu

March 20, 2023
Yanzu-Yanzu: Zanga-zangar Karancin Kudin Naira Tana Cigaba Da Yaduwa

DA DUMI-DUMINSA: Jam’iyyar APC Ta Lashe Zaben Gwamnan Jihar Ebonyi

March 20, 2023
Gwamna Umahi Ya Kori Wasu Mataimakansa Sa’o’i 48 Bayan Kammala Zabe

Gwamna Umahi Ya Kori Wasu Mataimakansa Sa’o’i 48 Bayan Kammala Zabe

March 20, 2023
INEC Ta Bayyana Wanda Ya Lashe Zaben Gwamna A Jihar Filato

INEC Ta Bayyana Wanda Ya Lashe Zaben Gwamna A Jihar Filato

March 20, 2023
PDP Ta Lashe Kujeru 28 Na Majalisar Dokoki, Yayin Da APC Ta Tsira Da Hudu

PDP Ta Lashe Kujeru 28 Na Majalisar Dokoki, Yayin Da APC Ta Tsira Da Hudu

March 20, 2023
Dan takarar LP Ya Taya Zababben Gwamnan Filato Murnar Lashe Zabe
Labarai

Dan takarar LP Ya Taya Zababben Gwamnan Filato Murnar Lashe Zabe

March 20, 2023
An bai wa hammata iska tsakanin Sojoji da Yan sanda, Jami’ai biyu sun mutu
Labarai

An bai wa hammata iska tsakanin Sojoji da Yan sanda, Jami’ai biyu sun mutu

March 20, 2023
Yanzu-Yanzu: Zanga-zangar Karancin Kudin Naira Tana Cigaba Da Yaduwa
Labarai

DA DUMI-DUMINSA: Jam’iyyar APC Ta Lashe Zaben Gwamnan Jihar Ebonyi

March 20, 2023
Dan takarar LP Ya Taya Zababben Gwamnan Filato Murnar Lashe Zabe

Dan takarar LP Ya Taya Zababben Gwamnan Filato Murnar Lashe Zabe

March 20, 2023
An bai wa hammata iska tsakanin Sojoji da Yan sanda, Jami’ai biyu sun mutu

An bai wa hammata iska tsakanin Sojoji da Yan sanda, Jami’ai biyu sun mutu

March 20, 2023
Yanzu-Yanzu: Zanga-zangar Karancin Kudin Naira Tana Cigaba Da Yaduwa

DA DUMI-DUMINSA: Jam’iyyar APC Ta Lashe Zaben Gwamnan Jihar Ebonyi

March 20, 2023

Twitter

Archives

Recent Posts

  • Dan takarar LP Ya Taya Zababben Gwamnan Filato Murnar Lashe Zabe
  • An bai wa hammata iska tsakanin Sojoji da Yan sanda, Jami’ai biyu sun mutu
  • DA DUMI-DUMINSA: Jam’iyyar APC Ta Lashe Zaben Gwamnan Jihar Ebonyi

Quick Links

  • Tsaro
  • Siyasa
  • Labarai
  • Wasanni
  • Kasuwanci
  • Rikicin Duniya

Contact Us

info@dimokuradiyya.com.ng

0809 912 4425 +234 809 912 4425

No. 218 Mogadishu layout Kaduna City Center Ahmadu Bello way kaduna. Kaduna, Nigeria 800273

Copyright © 2022 Dimokuradiyya Media Services LTD.

No Result
View All Result
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Rahotanni
  • Wasanni
  • Rikicin Duniya
  • Nishadi
  • More
    • Kasashen Ketare
    • Kiwon Lafiya
    • Ilimi
    • Kasuwanci
    • Noma Da Kiwo
    • Labarun Mako
    • Talla
    • Masarautu
    • Babu Maraya
    • Addini
      • Wa’azin Kirista
    • Girke-Girke
    • Waiwaye
    • Marubutanmu
    • Wasiku
    • Ni’ima Dai Mata
    • Tsaro
    • Bidiyo
    • Audio

Copyright © 2022 Dimokuradiyya Media Services LTD.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In