A girmama hakkin Nnamdi Kanu, Abaribe
Jagoran marasa runjayen Yan majalisu Enyinnnaya Abaribe ya shawarci gwamnatin tarayya dasu kula, kuma su kiyaye da hakkin Nnamdi Kanu.
Nnamdi Kanu Jagoran masu fafutukar kafa kasar BIAFRA, an kamashi sannan aka dawo dashi gida Najeriya aka gurfananar dashi a Kotu ranar Talata.
Dan majalisa Abaribe, dai shine wanda ya tsayama Nnamdi Kanu a lokacin da aka kamashi a shekarun baya. Kamar yadda Jaridar Punch ta ruwaito.
KARANTA:-Yan bindiga sun harbe wani Dan majalisa
Sa’annan ya Kara da cewa gwamantin tarayya dasuyi duba zuwa kundin mulkin 1999 a shafi na 31 na dokokin kasar Najeriya.
Ya cigaba da cewa gwamantin ta kara dubawa cikin atikul na 4 a kundin hakkin dan adam na afirika a lokacin da Nnamdi Kanu ke tsare a gidan kaso.
Abaribe yace yanzu aka fara shari’ar, ana iya cewa baida laifi har sai an tabbatar dashi.
Jagoran marasa runjayen yace “a kwantar da hankali kan abunda ya faru, sannan gwamnatin tarayya ta fito tayi bayani kan abubuwan da suke kawo rudani a kasar domin zaman Lafiya da hadin kai.