Shugaban Kwamitin Sojin Ƙasa na Majalisar Dattijai Sanata Ali Ndume yace matsalar tsaro na raguwa, inda yayi fatan cewa za’a gama da matsalar.
Ndume mai wakiltar Borno ta Kudu, y bayyana haka a lokacin da yake amsa tambaya daga ƴan jarida, bayan an naɗa ɗan takarar Shuwagabancin Jam’iyyar APC na Ƙasa Malam Saliu Mustapha a matsayin sabon Turakin Ilorin a ranar Juma’a.
“Matsalar Tsaro na raguwa, amma ba’a Gama da’ita ba, wannan wani abune da baza kace an gama da matsalar ba,” inji shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ƴan Sanda sun cafke mutane 3 da laifin tona gawar wani mutum a Jahar Ogun
Tsohon Shugaban masu Rinjayen yace Gwamnatin Tarayya na bakin ƙoƙarin ta, kuma a shirye take ta magance matsalar tsaro.
Dayake jawabi bayan an naɗa shi Mustapha yace yayi farin ciki aka bashi sarautar domin cigaba da bayar da gudummawa ga al-ummar.
Ya godema Sarkin Ilorin Alhaji Ibrahim Sulu Gambari daya bashi sarautar.