Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta hana makiyaya daga kasashen ketare shigowa Najeria saboda wannan ita ce hanya guda daya da za a kawo karshen takaddamar dake faruwa tsakanin manoma da makiyaya.
Ganduje ya bayyana haka ne a cikin wani jawabi da ya gabatar a ranar Asabar yayin bikin bude rukunin gidaje da wajen kiwo a dajin Dansoshiya dake kamarar hukumar Kiru da gwamnatinsa ta ginawa makiyaya da nufin kawo karshen yawon kiwo da suke yi.
Ya ce “dole ne a hana makiyayan ketare shigowa cikin kasar saboda suna shigowa da makamai wanda yake haddasa tarzoma a tsakaninsu da manoma”.
“Ko da kuwa an ga bayan annobar sarke numfashi, ya kamata a ci gaba da kulle iyakokin kasar nan musamman ga kasashen yammacin Afirika, domin samawa kasar nan tsaro”.
“Yawon da suke yi shi yake kawo sabani tsakaninsu da wasu al’ummar ba wai iya manoma ba”.
Ganduje yace gina musu wajen kiwo da kima matsugunni yana daya daga cikin shirin da gwamnatinsa ke yi na ganin ta kawo karshen rigicin dake faruwa tsakanin manoma da makiyayan.
Ganduje yayi alkawarin gina makaranta da asibiti domin mazauna wajen su damar samun kulawa ga lafiyarsu da kuma samun ilimi ga yaransu.
A lokacin da yake gabatar da jawabinsa Daraktan hukumar ruwa ta jihar Kano (WRECA) Mista Munir Gwarzo, yace hukumar tasa zata samar musu da ruwa mita miliyan biyu domin sama musu sauki wajen gudanar da kiwonsu, sai dai aikin da aka fara ya samu cikas sakamakon bullar annobar sarke numfashi.