Dan takarar shugaban Najeriya na jam’iyyar APC mai mulkin kasar, Bola Tinubu, zai gabatar da tsohon gwamnan Jihar Borno Kashim Shettima ga al’umar kasar nan a matsayin mataimakinsa a zaben shekarar 2023.
Wata sanarwa da jam’iyyar APC mai mulki ta kasa ta wallafa a shafinta na Tuwita ranar Talata da safe ta ce za a gabatar da Sanata Shettima ne, a gobe Laraba.
Sanarwar ta yi nuni da cewa, “A hukumance jam’iyyar APC za ta gabatar da dan takarar mataimakin shugaban kasarta, Sanata Kashim Shettima, ga al’ummar Najeriya ranar Laraba, 20 ga watan Yulin shekarar 2022.
Za a yi bikin gabatar da shi ne a babban dakin taro na Shehu Musa Yar’Adua da ke bababn birnin Tarayya Abuja da misalin karfe 11 na safe.
Idan ba’a nanta ba dai A makon jiya ne Bola Tinubu ya sanar da zaben tsohon Gwamnan Jihar Borno kuma Sanata mai wakiltar Mazabar Borno Ta Tsakiya, Kashim Shettima, a matsayin wanda zai yi masa mataimaki a babban zaben shekarar 2023 mai zuwa..
Sai dai awanni ashirin da hudu da fitar da sanarwar daukar Shattiman, batun ya jawo muhawara mai zafi inda wasu ke ganin bai dace Tinubu, wanda Musulmi ne daga yankin kudancin Kasar nan, , ya zabi Shettima, wanda Musulmi ne daga Arewacin Najeriya a matsayin mataimakinsa ba.
Amma jam’iyyar APC da ma Tinubu sun ce zabensa ba shi da alaka da addini.
Shettima gogaggen ɗan siyasa ne wanda ya daɗe yana jan zarensa a siyasa musamman a arewa maso gabashin kasar nan.
An haife tsohon ma’aikacin bankin a ranar 2 ga watan Satumbar 1966 kuma ya yi karatu a Jami’ar Maiduguri da kuma Jami’ar Ibadan.
A wani labarin kuma na daban.
Matsalar Tsaro: Gwamnatin Tarayya zata rushe Makarantun Kwana domin hana kai hare-hare a Makarantu
Gwamnatin Tarayya na shirin ajiye wasu sabbin Matakai na magance aikace-aikacen Ƴan Ta’adda da ƴan bindiga daga gudanar da mummunan ta’addancin su a Makarantu.
Babban Sakataren Ma’aikatar Ilmi na Kasa Mr. Andrew David Adejo ya bayyana haka a lokacin taron Kwamitin tuntuɓa na Ilmi karo na 81 daya gudana a ɗakin taro na Banquet dake gidan Gwamnatin Jahar Adamawa a ranar Litinin.
Mr. Adejo ya bayyana cewar wasu daga cikin matakan sun ƙunshi, shigo da Malamai da Ɗalibai akan harkokin tsaro, da rushe Makarantun Kwana, da ƙirƙirar ɓangaren tsaro na musamman a Makarantu, da sanya Na’urorin Ɗaukar Hoto na CCTV, da ɓullo da Darasi akan tsaro na manyan makarantu.
“Ya zama dole yadda ake samun kai hare-hare a makarantun ilmin mu, sace Ɗalibai, Malamai, da iyaye, wanda hakan na kawo tsaiko ga ɓangaren ilmi.
Yace taken taron wannan shekarar shine “inganta tsari da kare Makarantun Najeriya domin cimma nasarori da aka tsara zuwa shekarar 2030” nada manufar inganta koyo, tare da magance Ɗabi’a da halaye da lafiyar Makarantu.
Gwamnan Jahar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri wanda ya buɗe taron, yace Gwamnatin Jahar tuni ta gano yadda mahimmancin canja yanayin tsarin makarantu a Jahar.