A kwanaki sanannen marubucin nan Wole Soyinka, ya bayyana tsoronsa kan alámarin abin da zai iya biyo baya game da Fulani a Najeriya da abin da ya kira ”RUGA”.
Wannan magana tasa tana kara fitowa fili, yadda alámarin abin da hukumomi ke kira mamayar da Fulani ke yi da shiga hurumin manoma.
Jaridar Vanguard ta yau da safe, ta ruwaito cewa, a ranar Laraba da ta gabata, wasu gungun Fulani a Jihar Imo, sun yi ta harbe-harbe a sararin samaniya babu kakkautawa, a garin Obokofia a cikin jihar. Fulanin sun ce ba za su bi umarnin Gwamnati ba, na waádin da aka ba su na su bar wannan gari.
Ko a jiya ma, wata kotu a Abuja ta yi watsi da karar da Kungiyar Fulani ta Miyetti Allah ta kai Gwamnatin Tarayya suna kalubalantar dokar hana ciyar da dabbobi ciyawa na barkatai ta shekarar 2017, wanda Majalisar Dokoki ta Jihar Benue ta kai. Har ma an ji Gwamna Jihar Samuel Otom na fadin cewa wannan mataki da kotu na dauka babbar nasarar ce ga Demokradiyya.
A sakamaon zaman dar-dar din da ake yi a Jihar Imo, Shugaba kasa Muhammad Buhari ya yi zama da bangarorin tsaro a Aso Villa, da Kwamandan Mayakan Sama, Air Vice Marshal Sadiq Abubakar, yana jinjina musu tare da fadin matakan da Jamián tsaro suke dauka a kasar nan na magance taáddanci yana yin kyau sosai.
An ruwato cewa, tsohon Acrhibishop na Jihar Lagos Emiritus Anthony Cardidal Olubinmu, ya ce hakika yanzu Najeriya ta soma shiga cikakkiyar rigimar Fulani, saboda soke tsarin tsugunar da su da Gwamnatin tarayya ta yi.