Tawagar shiga tsakanin da ECOWAS ta aika zuwa Mali domin sasanta rikicin siyasar da yake aukuwar a kasar ta gabatar da tayin kafa gwamnatin hadin gwiwa a tsakanin gwamnati da ‘yan adawa. Sai dai ya zuwa yanzu babu bangaren da ya maida martani kan wannan tayin, wanda shi ne karo na biyu da tawagar dake karkashin tsohon shugaban Nijeriya, Goodluck Jonathan ke wannan yunkuri tun bayan soma aikinta a makon jiya.
A karshen makon ne kawancen ‘yan adawar na Mali ya yi fatali da tayin amincewa da nada sabbin Alkalan kotun tsarin mulkin kasar da aka rusa, don sake nazarin sakamakon zaben ‘yan majalisar da ya zama silar zanga-zangar kin jinin gwamnati da neman tilastawa shugaba Ibrahim Boubacar Kieta yin murabus.
A ranar Juma’a 17 ga watan Yuli ‘yan adawar suka ce babu gudu ba ja da baya kan sharadin da suka gindaya na neman murabus din shugaba Ibrahim Boubacar Kieta.