Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta Kano KAROTA ta ƙara cafke matashin nan mai suna Abdullahi Babakura wanda aka kama shi makwanni biyu da suka gabata da zargin yin amfani da Baburin Adaidaita Sahu yana satar wayoyin jama’a.
An kama Babakura ne a kan titin Kundila Maiduguri Road, lokacin da wani matashi mai suna Abdulhadi Isyaku ya buƙaci Babakura ya kai shi kan titin Kano Gest-in, dake karamar hukumar Fagge.
Bayan da suka ɗauke masa waya sai suka ce masa ba inda ya buƙata za su je ba, kamar yadda Abdulhadi ya shaidawa Hukumar KAROTA.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Makwanni biyu da suka gabata, Hukumar KAROTA ta ta cafke Abdullahi Babakura da aikata makamancin laifi irin wannan, inda aka miƙa shi a hannun ƴan sanda domin faɗaɗa bincike.
A binciken da KAROTA ta gudanar ta gano cewa bayan da ƴansanda suka gudanar da binciken sun gabatar da shi a gaban Kotu, inda ta yanke masa hukuncin zaman gidan gyaran hali ko zaɓin biyan tara.
Bayan ya biya tarar ne ya fito domin ci gaba da aikata makamancin laifin.
Babakura ya bayyana cewa ba shi kaɗai yake yin satar wayar ba suna yi ne tare da wani abokinsa mai suna Abbati Bright a inda da zarar sun ɗauki wayar Fasinja sai su ce ba inda ya buƙata za su je ba.
Hukumar KAROTA ta miƙa Abdullahi Babakura Sashen Binciken Manyan Laifuka na Rundunar ƴansandan jihar Kano domin faɗaɗa bincike.