Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, a karon farko a yau Larabar, ya halarci taron majalisar zartarwa ta tarayya da ya saba gudanuwa a Abuja.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa wannan shine karon karon Farko da ya bayyana, tun bayan da aka yi masa aikin tiyata cikin nasara a ranar 16 ga watan Yuli, a wani asibitin dake Ikejan jihar Lagos.
An yi masa tiyatar ne bayan karaya da ya samu a kafarsa, kuma raunin da ya samu a kafar tasa ya addabar shi, lamarin daya tilasta masa zuwa don ayi masa aiki.
KARANTA ANAN: SSANU, NASU Reshen UNILAG Na Zanga Zangar Adawa Da Janye Yajin Aikinsu
Osinbajo, wanda aka sallame shi a ranar 25 ga watan Yuli, yana samun murmurewa a gida kuma kusan yana halartar Wasu daga cikin ayyukan gwamnati.
Mataimakin shugaban kasar ya samu tarba daga ministoci da hadiman shugaban kasa a taron majalisar ministocin tarayya da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta.
Daukacin wadanda suka saba halartar zaman suma su halartar.
Ga wasu Daga cikin hotunan yadda ka is fadar shugaban kasar: