Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta kammala yarjejeniyar nada Mauricio Pochettino a matsayin sabon kocinta na dindindin a kungiyar. Kamar yadda Punch ta ruwaito.
Pochettino, mai shekaru 51, zai karbi aikin horar da kungiyar daga Frank Lampard a karshen kakar wasa ta bana.
KARANTA WANNAN LABARIN: Aikin Hajjin 2023: Gwamnan Kogi Ya Nada Amirul Hajji Na Jihar
Ya koma gasar Premier ta Ingila bayan da Tottenham Hotspur ta kore shi a watan Nuwamban shekarar 2019.
Pochettino, wanda ya buga wa Argentina wasa sau 20, ya koma aiki a watan Janairun 2009 tare da Espanyol, wanda ya buga mata wasa fiye da 250.
Gabanin kakar wasa mai zuwa, akwai babban aiki a gaban Pochettino saboda a halin yanzu Chelsea tana mataki na 11 a kan teburin EPL ba tare da lashe wani kogi a bana ba.
A wani labari kuma, Yanzu-Yanzu: IGP Ya Bada Umarnin Kame Mawaki Seun Kuti
Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Usman Baba, ya bayar da umarnin tsare mawakan Afrobeat, Seun Kuti, bisa zargin cin zarafin wani dan sanda a Legas.
IG din ya ba da umarnin gudanar da cikakken bincike cikin sauri kan musabbabin kai harin da kuma gurfanar da wanda ake tuhuma a kan haka.