By Abbas Yakubu Yaura
Majalisar dokokin jihar Bauchi ta koka da yadda makarantar sakandiren gwamnati da ke Baba Takko ta rikide zuwa maboyar miyagun kwayoyi da kuma cibiyar shan miyagun kwayoyi.
Majalisar ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta mayar da makarantar zuwa wurin karbar haihuwa, wanda hakan zai fi amfani ga mazauna yankin.
Mataimakin kakakin majalisar, Danlami Kawule, wanda yake wakiltar mazabar Zungur/Galambi, ya yi jawabi a yayin zaman majalisar bisa wasu muhimman al’amura na gaggawa ga jama’a, ya kuma jawo hankalin majalisar kan wannan mummunan ci gaba.
Sannan ya bayyana cewa, idan ba a shawo kan lamarin ba zai haifar da babbar barazana ga tsaro da kuma mazauna yankin da ma jihar baki daya.
Kawule ya roki majalisar da ta sanar da hukumomin gwamnati cewa a mayar da makarantar zuwa wurin karbar haihuwa ko kuma duk wani wurin da zai taimaka wa al’umma, maimakon a rufe makarantar.
A nasa jawabin shugaban masu rinjaye, Tijjani Aliyu, ya ce batun tsaro na bukatar a ba da dukkan kulawar da ya kamata.
Ya ba da shawarar cewa kwamitin tsaro na majalisar ya kamata ya tuntubi jami’an tsaro da na gwamnati da abin ya shafa domin a gane hakikanin abin da ke faruwa, yana mai nuni da cewa su fito da hanyoyin da za su baiwa majalisar damar daukar matakin da ya dace.
Shugaban majalisar, Abubakar Suleiman, ya umarci kwamitin tsaro na majalisar ya tuntubi ofishin sakataren gwamnatin jihar domin jin halin da ake ciki, lamarin da ya ce yana da matukar damuwa.
Makarantar Sakandaren Gwamnati da ke Baba Takko ta kasance a rufe a zamanin gwamnatin Isa Yuguda sakamakon rikicin da ya faru a can.