Shugaban kasa Muhammadu Buhari a yau Alhamis zai tashi daga birnin tarayya Abuja zuwa birnin Adis Ababa na kasar Habasha domin halartar taron kungiyar tarayyar Afrika AU karo na 36.
Taken taron kolin kungiyar ta AU shi ne “Karfafa aiwatar da yankin ciniki cikin ‘yanci na nahiyar Afirka (AfCFTA).
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Dumi-Dumi: Hukumar NECO Ta Fitar Da Sakamakon Jarabawar SSCE ta 2022
Buhari zai halarci taruka uku “Babban taro kan zaman lafiya da tsaro, sauyin yanayi da kuma yanayin siyasa a wasu kasashen yammacin Afirka.”
Wata sanarwa da mai taimaka wa shugaba Buhari kan harkokin yada labarai Garba Shehu ya fitar, ta ce na farko shi ne taron majalisar zaman lafiya da tsaro (PSC) na shugabannin kasashe da na gwamnatoci kan halin da ake ciki a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo (AUPSC High-Level AU), wanda zai jagoranci taron Shugaban kasar Afirka ta Kudu, a matsayinsa na shugaban majalisar gudanarwar kasar na watan Fabrairu.
Na biyu shi ne taron kwamitin shugabannin kasashe da gwamnatoci kan sauyin yanayi (CAHOSCC), wanda shugaban Jamhuriyar Nijar ke jagoranta a halin yanzu.
A gefen tarurrukan shekara-shekara na kungiyar AU, Buhari zai kuma halarci wani babban taro na ban mamaki na hukumomin shugabannin kasashe da na gwamnatin ECOWAS.
Shugaban na Najeriya zai gabatar da jawabai a wadannan tarukan tare da gabatar da jawabinsa na kasa a bude taron kolin, wanda ya hada shugabanin kasashen kungiyar AU da kuma wasu kasashe da ba na AU ba da kuma cibiyoyin kasa da kasa da suka amince da kungiyar ta AU a Addis Ababa.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Buhari zai samu rakiyar wasu Ministoci da wasu manyan jami’an gwamnati, zai dawo Abuja ranar Litinin 20 ga watan Fabrairu.
Wannan na zuwa ne a lokacin da ‘yan Najeriya ke cikin wani hali a karkashin karancin kudin Naira.
A wani labarin kuma, Da Ɗumi-Dumi: Buhari Ya Tsawaita Wa’din Amfani da Tsohuwar N200
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin tsawaita wa’adin tsohuwar takardar kudi ta naira 200 zuwa kwanaki 60 masu zuwa.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin da yake jawabi ga ‘yan Najeriya a wani shiri da aka watsa a fadin kasar kan yadda ake aiwatar da shirin na naira da aka yi wa kwaskwarima a baya-bayan nan wanda ya janyo karancin takardun kudi.