Ana zargin wani jigo a jam’iyyar APC mai neman tsayawa takarar gwamnan jihar Kano a 2023 Barau Jibrin da almundahana da kuma zamba a kasafin kudin kasar.
An kuma zarge shi da karkatar da kudaden jama’a zuwa aljihunsa, inda ya wadata ‘ya’yansa da wadannan kudaden ba bisa ka’ida ba.
Ana zargin Jibrin mai wakiltar Kano ta Arewa da yin amfani da ofishin sa a matsayinsa na dan majalisar dattawan tarayyar Najeriya wajen tafka magudin kasafin kudi tare da wadata kansa da ’ya’yansa ba bisa ka’ida ba.
Koke da kungiyar matasan Arewacin Najeriya (NYCN) mai dauke da kwanan watan 7 ga watan Oktoba 2021 kuma ta mika wa Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta yi zargin cewa Sanatan ya yi amfani da kamfanonin da aka yi wa rajista da sunayen ‘ya’yansa da mukarrabansa wajen aiwatar da ayyukan mazabu da dama wanda akayi aikin ba bisa doka ba kuma hakan bai dace ba.
Shugaban kungiyar ta NYCN, Isah Abubakar ne ya sanya wa takardar hannu,inda ta bayyana sunayen ‘ya’yan Sanatan, kamar haka, Zainab Jibrin,Shawal Jibrin da kuma Khalil Jibrin, a matsayin daraktocin kamfanoni masu zaman kansu, ta hanyar su ne suka karkatar da kwangilolin gwamnati tare da karkatar da kudaden gwamnatin.
A halin yanzu Sanata Jibrin shine shugaban kwamitin majalisar dattawa akan kasafin kudi.
Sannan takardar ta zayyana wasu daga cikin kamfanonin daya mallaka da kuma amfani dasu wajen karkatar da kudaden jama’a da suka hada da Sinti Nigeria Limited (RC 398938) da Engr.Jibril Power Electrical Engineering (BN 2431830), wanda a yanzu haka Yaransa ne daraktoci a kamfanoni.
Kazalika wasu daga cikin ‘ya’yansa kuma sun mallaki kamfanoni masu zaman kansu na kasuwanci.Misali, karar ta yi zargin cewa Khalil Jibrin ya mallaki kamfanin Talgo Luxury Estate Investment Nig Ltd (RC1312306), sai Zainab Jibrin wadda ta mallaki kamfanin Zajib Multi-Purpose Business Stores (BN2637321).
Takardar ta ci gaba da ba da cikakken bayani kan wasu kwangilolin da wadannan kamfanoni suka yi, wadanda akasarinsu sun samo asali ne daga gwamnati ta hannun sanatan.
Misali, kamar kwangilar kammala Cibiyoyin Karatu guda 13 a gundumar Sanata Kano ta Arewa, da aka kama a kasafin kudin 2020 mai lamba ERGP22582428 akan kudi Naira 430, 000,000 a karkashin ma’aikatar ilimi, wanda kamfanin Sanatan ne ya gudanar da shi aikin.
Masu shigar da kara sun yi imanin an samu kwangilar ne ta hanyar abokan huldar sanatan a matsayin shugaban kwamitin majalisar dattawa kan ilimin manyan makarantu a majalisar dattawa ta 8.
Bugu da kari, koken ya yi zargin cewa duk da rashin bin doka da aka bayar na kwangilar, aikin bai kammala ba duk da biyan kudin da gwamnatin tarayya tayi.
‘Za mu iya tabbatar da cewa an bayar da kwangilar ne ga kamfanin SINITI NIGERIA LIMITED saboda tasirin Sanatan, Tun daga lokacin an yi watsi da aikin,sai dai amma duk da haka gwamnatin tarayya ta biya kudin aikin,inda Sanatan dai ya karkatar da kudaden ne zuwa ga amfanin sa na kashin kansa domin cutar da mutanen Kano ta Arewa nagari,” inji takardar.
Kazalika Takardar ta kuma yi ikirarin cewa Jibrin ya cika kasafin kudin sakataren gwamnatin tarayya “domin hada kudin Naira 40, 000,000 ba bisa ka’ida ba tare da lambar kasafin kudi mai lamba ERGP86582461 domin gudanar da aikin jinya a gundumar Kano ta Arewa”.
Sannan yace “An saki kudaden ne a daidai lokacin da annobar cutar COVID-19 ke yaduwa, musamman a lokacin kullen kasa baki daya da kuma lokacin da jami’an kiwon lafiya suka yi yawa kuma suka kasa fara aikin jinya. Kudaden dai tuni Sanatan da mukarrabansa suka yi ta nishadi.”
Karin zargin sun hada da cewa “Sanatan ya kuma ci gajiyar kwangilar aikin gyara Dam na gundumar Getso Kano ta Arewa, wanda aka kama a cikin kasafin kudin shekarar 2020 mai lamba ERGP 22583468 a karkashin ma’aikatar albarkatun ruwa.
“Biyan maɓalli na uku da aka biya shi ne Naira miliyan 16,000, 000 na gyaran dam wanda Har yanzu dam din na cikin rugujewar Babu wani gyara da akayiwa madatsar.
“Mun kuma damu matuka cewa Sanatan da ‘ya’yansa a halin yanzu suna da tarin dukiya da ta zarce kudin shigar da Sanatan ke samu. Sannan “Mun yi imanin cewa hukumar tana da kayan aiki da kwarewa don gano dukiyar da kuma mayar da su cikin asusun gwamnati inda take,” in ji ta.
Takardar ta kuma yi zargin cewa Sanatan ya samu koma-baya ta hannun ‘ya’yansa da kamfanoninsu na bogi, inda tace kamfanin Talgo Luxury Estate Investment Nig Ltd yana da adireshi mai rijista a jihar Neja yayin da Zajib Multi-Purpose Business Stores ke da adireshin rajista a jihar Kogi.
Kungiyar ta kara da cewa “Ba sa gudanar da wasu manyan sana’o’i da ke bayar da cikakun miliyoyin da suke ajiyewa a asusun ajiyarsu na banki.”
Wani na hannun daman Sanatan daya ki a bayyana sunansa ya ce dan siyasar bai aikata wani laifi ba ta hanyar mallakar kamfanoni masu zaman kansu. Ya kuma ce ‘ya’yan Sanatan ‘yan Najeriya ne da ke da ‘yancin gudanar da sana’o’insu daban-daban.
“Game da zargin karkatar da dukiyar jama’a, wannan iƙirari ne kawai wanda ba a tabbatar da shi ba,” in ji shi.