Cibiyar dakile cututtuka masu yaduwa ta Nijeriya, NCDC ta tabbatar da cewa an kara samun mutum 117 da suke dauke da cutar Koronabairos a Nijeriya.
Wannan adadin ya sanya yanzu NIjeriya na da mutum 782 da suke da Korona a fadin kasarnan.
Sabbin wuraren da aka samu masu Korona sun hada da; 59 daga Legas, 23 a FCT, 14 a Kano, 6 a Borno, 4 a Kastina , 3 a Ogun, sai guda daya-daya daga Rivers da Bauchi.
A sakon da suka wallafa a shafinsu na Twitter, NCDC sun ce ya zuwa yanzu masu cutar sun kai 782, a yayin wadanda suka warke sun kai 197, sai kuma wadanda suka rasa ransu guda 25.