Jihar Kano ta samu mutum 40 masu dauke da cutar korona a rana daya, wanda hakan ya sanya a yanzu masu dauke da cutar sun kai 318.
Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano din ta tabbatar da hakan a sakon da ta wallafa a shafinta na Twitter a ranar Talata.
Har wala yau ma’aikatar lafiyar ta ce mutum 48 da suka warke daga cutar cikin awa 24 an sallame su.
Ma’aikatar lafiyar ta ce sun yi wa mutum 58,765 gwajin cutar, inda aka samu mutum 2,364 da cutar, aka kuma sallami 1,978.
Ya zuwa yanzu mutum 68 ne kawai cutar ta kashe a fadin jihar tun bayan bullar cutar.
Ma’aikatar ta nemi al’ummar jihar da su rika bin dokokin kariya daga kamuwa da cutar domin dakile yaduwar cutar.