A rana mai kama ta yau wato 13 ga watan Satumba na shekarar 1989 aka haifi ɗan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayern Munich kuma ɗan asalin ƙasar Jamus wato Thomas Muller, wato yau kenan ya keyin bikin murnar zagayowar ranar haihuwarsa.
An hafi Muller a garin Weilheim Oberbayern dale yammacon ƙasar Jamus inda a halin yanzu yana da shekaru 31 a duniya kenan, Muller dai yazo Bayern Munich a shekarar 2000 wato ƙaramar ƙungiya ta 3 wato C kenan, sannan kuma ya koma Bayern Munich B a shekarar 2008 zuwa 2009 inda ya buga wasanni guda 35 yaci ƙwallaye 16.
Muller ya shigo babbar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayern Munich a shekarar 2009 zuwa yanzu sannan ya bugamusu wasanni 351 ya jefa ƙwallaye guda 118. Haka ya bugawa babbar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Jamus wasanni 100 yaci ƙwallaye 38 daga 2010 zuwa yanzu.
Ga jerin kofunan daya lashe:
Ya lashe gasar Bundes Liga guda 9.
Ya lashe gasar ƙalu-bale ta Jamus guda 6.
Ya lashe gasar Germain Super Cup guda 5.
Ya lashe gasar zakarun nahiyar turai guda 2.
Ya lashe gasar European Super Cup guda 1.
Ya lashe gasar zakarun nahiyoyi guda 1.
Dukkanin kofunan da aka lissafa ya lashesu ne tare da Bayern Munich.
A matakin ƙasa kuwa wato Jamus ya lashe gasar cin kofin duniya sau 1 a shekarar 2014 da ƙasar Brazil ta karɓi baƙunci.