Daga Umar El’faruk Nasarawa
Mai girma gwamnan jihar Nasarawa Injiniya Abdullah A. Sule ya ziyarci makarantar Nakasassu dake Lafiya fadar gwamnatin jihar.
Wannan dai shi ne ziyara ta farko da gwamnan ya kai bayan shan rantsuwar kama aiki a jiya laraba 29-05-2019
Ya bayyana jin dadin sa bisa game da yadda hukumar makarantar suke gudanar da ayyukan su.
Ya kara da cewa, wannan makaranta tana da matukar mahimmanci a gare ni, dan haka zan yi kokarin ganin an kara daukaka darajar koyarwar da ake yi a makarantar ya zama tana gogayya da sauran kasashen Duniya.
Daga karshe hukumar makarantar sun bayyana jin dadin su da zaben makarantar a matsayin ziyayar farko a hukumance da gwamnan ya fara.