Daga Usman Salisu Gurbin Mikiya
Masu kiwon kaji a Kano, sun yi asarar makudab kudade har sama da Naira milyan 600, bayan da cutar murar tsuntsaye ta bulla a gonakin kiwon kaji 42 a cikin watanni 2 da suka shude.
Shugaban kungiyar masu kiwon kaji reshen jihar Kano Umar Usman Kibiya ya tabbatar da hakan ga manema labarai a Kano.
Yace watanni biyu da suka shude masu kiwon kajin suka kai rahoton bullar cutar ga mahukunta, bayan da suka ga alamun cutar ga kajinsu.
Umar Usman yace tun wancan lokacin, kungiyar da jami’ai daga ma’aikatar aikin gona ta jihar suke ta fadi tashin ganin an yaki cutar.
Shugaban kungiyar masu kiwon kajin ya shaida wa Daily Trust cewa ya zuwa yanzu gonakin kiwon kaji 42 ne lamarin ya shafa, ya kara da cewa an dauki samfurin 40 domin yin gwaje-gwaje.
Ya kuma shaida cewa jami’an sun yi nasarar kwashe kaji sama da dubu 223, a gonakin da lamarin ya faru.