Ƙungiyar haɗin kan malaman Kano ta ce tana nan kan bakanta na yin muƙabala da Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara.
Sanarwar da ƙungiyar malaman ta aike wa BBC ranar Asabar ta ce ta bi umurnin kotu na dakatar da muƙabalar da aka shirya yi ranar Lahadi 7 ga watan Maris.
Amma sanarwar ta ce da zarar kotu ta amince za a yi muƙabalar domin ƙalubalantar Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara.
A ranar Juma’a ne kotu a jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta dakatar da yin muƙabala tsakanin Sheikh Abduljabbar da malaman na Kano da aka shirya yi.
Kotun ta yanke hukuncin sakamakon buƙatar da wani lauya mai zaman kansa Barista Ma’aruf Yakasai ya shigar gabanta.
Barista Yakasai ya buƙaci a dakatar da gwamnati daga yin muƙabalar ne, saboda hakan ya ci karo da umarnin da kotun ta bayar tun da fari na hana Sheikh Abduljabbar karatu da kuma saka karatunsa a daukacin kafofin yada labaran jihar.