Ma’aikatar lafiya ta Nijeriya, ta ce a shirye take ta hada hannu da daidaikun mutane ko kungiyoyi domin samar da kayayyakin lura da lafiya a kasarnan.
Sanata Adeleke Mamora, ministan ma’aikatar lafiyar ne ya tabbatar da hakan a sanarwar da mafaimakin Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar wato Ms Eunice Akro ya fitar a birnin tarayya Abuja a ranar Litinin.
Mamora ya bayyana hakan ne a yayin da tawagar ‘USAID Global Health Supply Chain Program-Procurement and Supply Management (GHSC-PSM)’ a Nijeriya a karkashin kulawar shugabanta na Nijeriya, Mike Egboh ya jagoranta suka kai masa ziyara.
Ministan ya bayyana matakan gwamnati na kulla alaka da kungiyoyi wajen bunkasa bangaren lafiya a Nijeriya.