Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce, a shirye yake ya yi aiki tare da Sanatan da ke wakiltar Kano ta Tsakiya kuma tsohon gwamnan jihar, Malam Ibrahim Shekarau, kafin shekarar 2023.
Ya kuma ce bai yi mamakin rikicin da ke ruruwa a jam’iyyar APC mai mulki a Kano tsakanin gwamna Abdullahi Umar Ganduje da sanatan ba.
Da yake magana a wata hira da BBC Hausa, jigon na Jam’iyyar PDP ya ce, “Duk wanda ba zai iya rama abubuwan alherin da aka yi masa tsawon shekaru ba, saboda shi da kansa (Ganduje) ya ambata cewa, mun yi abubuwan, Kuma mutane da yawa sun shaidan hakan.
“Amma lokacin da ya hau karagar mulki, ba zai iya yi wa Kwankwaso da mabiya Kwankwasiyya alheri daya ba. To ta yaya kuke tsammanin zaman lafiya zai kasance a wurin? Na san yana zuwa, lokaci ne kawai, ”in ji shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan sanda sun Kwato Manyan Makamai wurin Yan bindiga
Da yake mayar da martani kan rahotannin da ke cewa Shekarau ya yaba masa, Kwankwaso ya ce, ya ji dadin kalaman.
Dangane da ko za su ci gaba da zama a sansanin siyasa ɗaya, Kwankwaso ya ce, ba zai yi mamaki ba domin idan Allah ya ƙaddara hakan ta faru, toh tabbas sai ta faru.
Tsohon ministan tsaro ya bayyana cewa, ya yi shiru a PDP saboda rashin adalcin da aka yi wajen zaben shugabanni a reshen Kaduna na jam’iyyar.
Ya Kuma Kara da cewa, bayan sun gudanar da zaben, wasu daga cikin shugabannin son kai sun yanke shawarar haifar da matsaloli ga shugabancin Kano, wanda a cewarsa, an warware su matsalolin daga bisani.
Amma ya ce, ya ci gaba da kasancewa dan PDP har izuwa wanna lokaci.
Idan za’a iya tunawa dai, Shekarau ya gaji Kwankwasoe a matsayin sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya a majalissar Dattijan kasar nan.
Comments 1