A wannan dare na Talata za a rufe kaauwar hada-hadar sayen ‘yan wasa amma a gasar zari-ruga da za a fara gudanarwa musamman a nahiyar turai.
Tuni dai aka fara cinikayyar ‘yan wasan na zari-ruga kuma ya zuwa yanzu wasu kungiyoyin masu dabara har sun sayi manyan ‘yan wasa domin yin garambawul a inda suke da matsala.
Itadai wannan gasa majiya ƙarfi ne suke yinta kuma wasa ne da akeyin gumurzu sosai yadda ya kamata kuma ana saurin jin ciwo ako wanna hali da yanayi ake ciki.
Wannan gasar dai nan da wasu kwanaki za a fitar da yadda za a fara fafata gasar rukuni-rukuni ta ƙasashe da dama inda kuma wasannin na bana zasu ƙayatar duba da yadda kowacce take tayin garambawul.