Akalla mutane bakwai ne rahotanni suka ce wasu ‘yan bindiga dauke da makamai sun kashe a wasu hare-hare daban-daban a wasu kananan hukumomi uku na jihar Kaduna.
Kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, ya tabbatar da faruwar harin a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.
Kananan hukumomin da abin ya shafa a cewar kwamishinan sun hada da Igabi, Chikun da Zango Kataf.
Ya bayyana cewa an kashe mutum hudu yayin da daya kuma ya samu raunuka a ranar Asabar da ta gabata, inda ‘yan bindiga suka kai hari kauyen Kerawa da ke karamar hukumar Igabi inda suka yi ta harbe-harbe.
Mutum daya ya samu munanan raunuka yayin da ‘yan bindigar suka kwashe wasu babura da kayan abinci na al’umma.
A wani lamari makamancin haka, wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane biyu a wasu hare-haren da suka kai a kananan hukumomin Igabi da Chikun.
Wata mata da harbinsu ya sameta ta mutu nan take yayin da wani mutum kuma aka harbe shi a kauyen Ungwan Zallah da ke karamar hukumar Chikun a jihar.
An kuma kai wa matafiya hari a wani lamarin da ya faru a kan hanyar Ungwan Rimi zuwa Afana a karamar hukumar Zangon Kataf kuma an kashe mutum daya.