Kafa mummunan tarihi a duniyayar ƙwallon ƙafa ba sabon abu bane ga dukkanin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafan da suke fafata wasanni a faɗin duniyar nan kama daga abin da ya shafi ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa dama ƙasashen da suke fafata sauran wasannin ƙwallon ƙafa kama daga nahiyar Afrika da nahiyar Asia da nahiyar turai da nahiyar Latin da sauran nahiyoyin duniya.
Ga wasu misalai da suka faru akan wasu ƙungiyoyin ƙwallon ƙafan idan mun ɗauki ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Juventus inda ta fafata wasannin ƙarshe na gasar zakarun nahiyar turai amma kuma bata lashe ba, Juventus dai tunda take a duniya tafi kowacce ƙungiya zubar da wasan ƙarshe na gasar zakarun nahiyar turai, ta buga wasannin ƙarshe sau 9 amma kuma sau biyu kawai ta lashe gasar inda ta ɓarar da guda 7. Kuma a halin yanzu babu abin da Juventus takeson taga ta lashe kamar gasar zakarun nahiyar turai.
Haka zalika idan muka dawo kan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal ita kuma kusan dukkanin watan Janairu na kowacce shekara Arsenal taka sami kanta a cikin tsaka mai wuya duba da irin yadda ake ragargazarsu inda kuma wani lokacin ko wasa guda basa iya ci a cikin watan, haka zalika wani lokacin koda sune suke jagorantar teburin gasar ajin Firimiya ta ƙasar Ingila akan sakko da ita da gaggawa duba da irin dukan da ake yimata a watan na Janairu.
Itama haka ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United kusan dukkanin wani mummunan rashin nasara data saba yi takan yine a watan Oktoba inda shekaru ta dama sun nuna cewar akan zubamusu ƙwallaye da dama a raga a gasanni daban-daban misamman a gasar ajin Firimiya ta ƙasar Ingila. Sai dai wannan abin rashin daɗi ya taso tsohon tsumi ne ganin yadda ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Tottenham ta caskara Manchester har gida daci 6 da 1.
Jaridar www.dimokuradiyya.com.ng ta zaƙulo wasu manyan rashin nasara da Manchester United ta dinga yi a baya kuma a cikin watan na Oktoba.
Ga jerin irin rashin nasarar da Manchester United ta dinga a cikin watan na Oktoba:
1. A watan Oktoba na sherara 1996 ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Newcastle United ta lallasa ta lallasa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United daci 5 da nema.
2. A watan Oktoba na shekarar 1999 ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea ta wanke Manchester United daci 5 da nema.
3. Haka zalika a watan Oktoba na shekarar 2011 abokiyar hamayyar Manchester United wato Manchester City ta ragargaza Manchester United daci 6 da 1.
4. A yammacin jiya itama ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Tottenham ta tumurmusa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United har filin wasa na OldTraford ƙarƙashin jagorancin mai horas wa Jose Mourinho daci 6 da 1.
Sai dai wannan rashin nasara da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United tayi yasa magoya bayanta na sassa daban-daban na duniya shiga cikin tararrabi na ganin cewar ƙarshen Manchester United yazo duba da yadda kowacce ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta kashe manyan kuɗaɗe amma ita Manchester bata kashe ta sayo ‘yan wasa ba.