Gwamnatin Ƙasar Amurka tace tana saran Gwamnatin Tarayya zata yi amfani da jiragen yaƙi na Super Tucano kaɗai a Arewacin Ƙasar, inda Ƴan ta’addan Boko Haram, suka maida yankin wajen kashewa Nigeria ƴan Ƙasar ta na tsawon fiye da shekaru goma, tare da kashe dubunnan mutane da korar Miliyoyin daga gidajen su.
Amma kuma bama saran Gwamnatin Tarayya zata yi amfani da jiragen a yankin Kudu maso Gabas, duk da ƴan ta’addan ƙungiyar ƴan awaren inyamurai ta IPOB sun yi cincirindo a Yankin, tare da ƙirƙirar jami’an tsaron su na ESN.
Yankin Kudu maso Gabas nan ne cibiyar ƴan awaren fita daga ƙasar Nigeria.
KARANTA WANNAN LABARIN: Bauchi: Rundunar ‘Yan Sanda Sun Cafke Mutane 19 Da Ake Zargi Da Aikata Laifuka Daban-daban
Dayake jawabi ga Manema labaru a farkon mako, mataimakin mai ba Ƙasar Amurka Shawara akan tsaro Jonathan Finer a taron da wakilin Najeriya ya halarta Mary Beth Leonard, yace ƙa’idojin da aka sanya a lokacin yarjejeniyar sayar da jiragen Tucano guda 12 an taƙaita su, koma akwai buƙatar cika su.
Dayake maida jawabi akan ko za’a iya amfani da jiragen Tucano ga ƴan awaren Kudu maso Gabas, Finer yace jiragen suna da matuƙar amfani wajen tabbatar da tsaro, musamman a yankin Arewa, inda ya bayyana rashin jindaɗi akan kasa tabbatar da cika sharuɗɗan yarjejeniyar.
Finer yace “ina tunanin mun faɗi yadda za’a yi amfani da jiragen nan, da inda ya kamata ayi amfani dasu, muna jin rashin jindaɗi, kuma muna fuskantar irin waɗannan matsaloli na tsaro a duk inda muka yi yarjejeniya a faɗin duniya.