Za a fara jigilar kashin farko na maniyyata 400 daga jihar Kano zuwa kasar Saudiyya don gudanar da aikin hajjin bana, wanda jigilar zata fara gudana ne a yau Litinin.
Babban Sakataren Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Abba Danbatta ne ya bayyana haka ga manema labarai yau a Kano.
Ya ce, “Idan duk shirye-shiryen suka tafi yadda aka tsara, a yau (Litinin) za a fara jigilar alhazan Kano zuwa kasar Saudiyya ta jirgin Azman Air, tuni alhazan suka shirya suna jiran a kai su kasa mai tsarki.
“Kamar yadda kuke gani, tuni alhazai sun je sansanin Hajji; Jami’an mu suna gudanar da gwajinsu na karshe da gwajin COVID-19, wanda ya zama tilas kafin tashin jirgin.”
Danbatta ya bada tabbacin hukumar zata fara jigilar maniyyatan.
An fara jigilar alhazai ne bayan da aka tsara tun daga ranar da aka shirya gudanar da aikin, duk kuwa da cewa tuni maniyyata daga wasu jihohin suka isa kasa mai tsarki.
Majiyoyi daga hukumar sun ce an samu tsaikon ne sakamakon matsalar da hukumar ta samu da kamfanin.
“Amma a wannan karon an shawo kan matsalar. Akwai tabbaci daga kamfanin jirgin cewa za mu fara tashi daga yau Litinin”, in ji daya daga cikin majiyoyin.