Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya shawarci jam’iyyun siyasa da ‘yan takarar da suka tsaya zaɓe a jihar Edo da su guji ɗabi’ar nan ta ko-a-mutu ko-a-yi rai a yayin zaɓen gwamnan jihar da za a gudanar a gobe Asabar.
Shugaban ƙasa Buhari ya aikewa musu cewa kaɗa ƙuri’a da ‘yan siyasa da jami’an tsaro da su kiyaye abinda zai haifar da rikici a zaɓen.
Wata sanarwa da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai Malam Garba Shehu ya fitar na cewa shugaba Buhari na fatan ganin an gudanar da zaɓe cikin kwanciyar hanakali da lumana tare da bin doka.
Sanarwar ta ce Buhari ya jaddada ƙudirinsa na ganin ana gudanar da mulkin dimokraɗiyya cikin tsari a ƙasar nan wanda hakan ba zai samu ba har sai ‘yan siyasa sun bada gudunmawa.