Wani dan Ghana ya koka kan yadda ‘yan matan Najeriya ke tatsar kudin samari da zarar sun fara soyayya da mutum.
A cewar mutumin mai suna Breggle Acha Derrick a wata wallafar da yayi a Twitter ya ce yanzu soyayya da matan Najeriya babban aiki ne kuma mutum na rasa ko soyayya ko kuma neman taimako suke yi.
KU KARANTA: Saboda diri na maza ke baro garuruwa don cincirindon siyan abincina, Budurwa
Ya ce soyayya da matan Najeriya ta yi kama da kulawa da maraya. Breggle ya kara da cewa da zarar tsautsayi ya ratsa da mutum yace yana son su; daga nan za su fara kawo matsalolin kudinsu.
Kamar yadda ya wallafa:
“Soyayya yanzu ta cude saboda baka san ko taimako ko soyayya mutum ke nema ba. Na ji labarin cewa yanzu soyayya da matan Najeriya kamar kulawa da maraya ne.”
Yadda saurayi ya rabu da budurwarsa saboda ta yi masa miya da bagen tumatur
Wata hira tsakanin saurayi da budurwa ta kacame inda saurayin ya rabu da budurwarsa kan ta yi masa miya da bagen tumatur kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.
Matashi ya tura budurwarsa kasuwa inda ya bukaci ta yi cefanen kayan miya wanda bayan ta dawo ta gane cewa cikin tumaturan akwai lalatacce.
Saidai a haka ta hada da shi tayi miyar wanda saurayin nata bai nuna damuwarsa ba inda ya dinga tunanin cewa ko an yi miyar ba za ta shafi dadin abincin ga.