Dan takarar gwamnan jihar Kano a jam’iyyar (NNPP), Abba Kabir Yusuf, ya nesanta kansa daga wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta na yanar gizo yana mai cewa ya amince da wasu tarin kudin da aka tara masa, inda kowa ya bayar da naira 1,000 daga wasu masu sha’awa da kuma ‘yan majalisar tarayya.
A wata sanarwa da mai magana da yawunsa Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, dan takarar gwamnan ya bukaci al’ummar Kano musamman ‘yan jam’iyyar NNPP da su yi watsi da faifan bidiyon.
KARANTA ANAN: Farashin Gas Ya Karu Sama Da Kaso 100 A Shekarar 1 – NBS
Ya bayyana faifan bidiyon a matsayin wani kamfe ne kawai na katsalandan da wasu mugayen jama’a da ke cikin ‘yan bangar siyasar adawa suka shirya.
Sanarwar ta kara da cewa, “Dan takararmu yana so ya bayyana karara cewa bai taba kaddamar da wani kudi a kan ayyukan yakin neman zabensa na 2023 da har yanzu ba a kammala ba.
“Ya kamata a lura cewa dan takarar ya san akwai abokan Abba Gida Gida a matsayin gungun abokansa na jami’o’in Najeriya daban-daban da sauran manyan jami’o’i da kwararrun shari’a da kuma ‘yan kasuwa da suka shirya kansu da nufin kawai, na inganta shugabanci nagari da dimokuradiyya wanda a cikinsa suka samu (Abba Gida Gida) jakadan da ya cancanta.”
“Mun tsaya tsayin daka kuma mun jajirce wajen ganin mun ceto jihar Kano daga halin da al’ummar jihar suka tsinci kansu a karkashin jagorancin da bai dace ba.”
A wani labarin kuma: Yajin Aikin ASUU: NANS Ta Dakatar Da Zanga Zanga A Legos
Kungiyar dalibai ta kasa NANS ta dakatar da zanga-zangar da ta shirya yi a Legas a yau Talata, don nuna takaici da ci gaba da rufe jami’o’in.
Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito yadda daliban suka ci cincirundo a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Legas a ranar Litinin.
Matakin da daliban suka yi ya jawo wa matafiya da masu ababen hawa fuskantar wahala domin an fuskanci matsalar cunkoson ababen hawa a sassa daban-daban na jihar.