Abba Kyari: Yadda Na Ɓoye Daga Ƴan Ta’addan Da Suka Kai Hari Gidan Yarin Kuje
Dakataccen Mataimakin Kwamishina DCP Abba Kyari ya bayyana yadda ya ɓuya daga ƴan ta’addan da suka kai hari cibiyar Kuje da ke Abuja.
A ranar 5 ga watan Yuli, ƙungiyar Boko Haram da ta balle daga yankin yammacin Afirka (ISWAP), ta jagoranci kai hari a cibiyar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zan Mayar Da Martani Ga Kalaman Ka Lokacin Dana Mika Muku Mulki A 2023 – Buhari Ya Fadawa Shettima
Da yake magana ta bakin Onyekachi Ikpeazu, lauyansa, a ranar Laraba, Kyari ya roƙi wata babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da belinsa.
“Ubangiji, duk mai rai a ƙasar nan zai yarda cewa ba wai an samu ɓaraka ba ne, a’a akwai wani babban harin ta’addanci da wata kungiya ta kai wanda ba wai kawai ta yi nasarar mamaye gidan yarin na Kuje ba, amma ta ƙwace shi sama da sa’o’i uku.
“Idan akwai wani abu da zai tabbatar da cewa wanda ake tuhumar zasu iya guduwa da tuni ya gudu. An bar Ƙofar gidan yarin a bude sama da awanni uku.
“Hakika wanda ake tuhumar ya ɓoye kamar ɓera, domin kungiyar da ta kai harin ta bi cell zuwa cell, inda ta ce suna so su kai shi da sauran su jeji.
Ban san a ina a duniya ba, inda ɗan sandan da aka ba da shaida kanshi, mai sadaukar da rayuwar sa, wadanda suka jefa rayuwarsu cikin hadari, suka bar iyalansu don yi wa ƙasa hidima, suna zaune a guri ɗaya da masu aikata laifuka guda ɗaya da suka sa aka kama su, inda wasunsu ke fuskantar hukuncin kisa.
Gwamnatin Tarayya ta ce fursunoni 879 ne suka tsere, ciki har da ƴan Boko Haram 68 da ke ɗaure a gidan yari.
Kyari da sauran jami’an Rundunar Ƴan Sandan IRT, ta hannun lauyansu, sun shaida wa mai shari’a Emeka Nwite cewa rayuwarsu na cikin haɗari a gidan yari.
Da yake gabatar da bukatar neman belin Onyechi Ikpeazu, SAN, wanda ya bayyana a karo na 1 (Kyari), na 4 da na 5, ya ce bayar da belin wadanda yake karewa ya zama dole domin rayuwarsu ba ta da lafiya inda a halin yanzu ake tsare da su.
Ya ce jami’an da suka yi kyakkyawan aiki a sana’arsu ta hanyar Damƙe miyagu masu haɗari da manyan mutane, wadanda galibinsu suke gidan yari daya tare da su, bai kamata a ajiye su a gidan ba.
Ikpeazu ya buƙaci Kotun da ta amince da bada belinsu bisa sharuɗɗan sassauci.
Haka kuma, Gboyega Oyewole, lauya mai kare wanda ake kara na 2, ya yi magana a irin wannan hali.
Sai dai lauyan hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa NDLEA, Sunday Joseph, ya ƙi amincewa da lauyan dake kare wanda ake ƙara. Ya bukaci kotun da ta yi watsi da bukatar neman belin.
Mai shari’a Nwite ta dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 30 ga watan Agusta domin yanke hukunci.
Tun da farko a shari’ar, lauyan NDLEA, Joseph, ya bayar da dala 61, 400 da ake zargin DCP Abba Kyari da aka dakatar ya yi amfani da shi wajen ba wa jami’in hukumar cin hanci da rashawa a karar da aka shigar da shi da wasu jami’an ƴan sanda hudu.
Joseph ya gabatar da kudaden ne a gaban kotun da aka bude a gaban alkali lokacin da mai gabatar da kara na uku, Peter Joshua, ke jagorantar shari’ar da aka dakatar da mambobin IRT.
A ci gaba da shari’ar, Joshua, wanda ke aiki a hukumar NDLEA, babban birnin tarayya Abuja a matsayin jami’in baje kolin, ya shaida wa Kyari da mutanensa.
Mai shari’a Nwite ta amince da kudin ne a shaida a matsayin nuni na 11 bayan lauyan da ke kare ya ki amincewa da bukatar.
NAN ta ruwaito cewa hukumar ta NDLEA ta yi zargin cewa tana da hujoji na hoto da bidiyo a kan dakatarwar shugaban hukumar ta Intelligence Response Team, DCP Kyari, wanda ya yi shawarwarin sakin hodar ibilis mai nauyin kilo 25 daga hukumar a Abuja