Gwamnatin jihar Kogi ta ware wasu wurare da ka iya fuşkantar ambaliyar ruwa don tilasta wa mazauna yankin barin wuraren, a wani yunkuri na gujewa sake afkuwar ambaliayr ruwa a jihar, ganin yadda Kogin Niger ke kara tumbatsowa.
Babban sakataren Obani Sunday a cikin wata sanarwa da ya baiwa manema labarai ya ce, alamominn ambaliyar ruwa sun kara baiyana ganin yadda yawan rowan kogin ke karuwa
Acewarsa, ganin irin barazaar ambaliyara ruwa da yankın ke fuskanta a nan bada jimawaba, za a umarci mazauna yankin su tashi su koma sansanonin da aka samar musu, domin ganın an dauki matakan daka iya kauce wa yin asarar rayuka da dukiyoyin Al’uma.
A cikin sanarwar Sunday ya nuna nadamuwar sa, ganin yadda matakin da gwamnatin jihar ta dauka Bai wa wasu mutanen yankin Dadi ba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Direbobin Tirela sun toshe Babbar Hanyar Bida a Niger
Kazalika rahotanni sun nuna cewa, wasu daga cikin al’umar yankin, sun ki bin umarnin gwamnatin Jihar Kogi, na koma wa cikin garin Lokoja babban birnin jihar, don samun tsira da rayuwar su.