Tsohon Shugaban Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Adams Oshiomhole, ya bayyana abin da zai yi idan magoya bayan jam’iyyar Labour Party, LP, da Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa, Peter Obi suka zo farmakar sa.
Oshiomhole ya bayyana cewa zai mayar da martani idan mabiyan Obi da aka fi sani da Obi-dients suka nemi yi masa martani.
Oshiomole yayi magana ne yayin da yake bayyana a shirin Arise TV, The Morning Show a ranar Laraba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamna Ganduje Zai Bar Najeriya, Bayan Ya Naɗa Gawuna a Matsayin Mukaddashi
Ya kuma yi nuni da cewa mafi yawan ‘yan takarar Shugaban Ƙasa ba su isasshe su sanar da ‘yan Nijeriya yadda za su warware matsalolin da ke addabar kasar ba.
Da yake nuna Obi, Oshiomole ya ce har yanzu Tsohon Gwamnan Jihar Anambra bai gayawa ƴan Najeriya yadda zai tunkari ƙalubalen kasar ba.
A cewar Oshiomhole: “An tambayi Obi ta yaya, sai ya ce, “Wannan sirri ne.”
Lokacin da aka gaya masa cewa magoya bayan Obi za su iya farmakar sa saboda sukar Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na LP, Oshiomole ya amsa da sauri: “Zan zo bayansu.”
An zargi magoya bayan Obi na yanar gizo da zage-zage ga wadanda ke adawa da aniyarsa ta Shugaban Ƙasa.