Akalla ‘yan Nijeriya Uku da wadansu ‘yan kasashen waje aka raunata a wani sabon rikici na kyamar baki da ya barke a kasar Afrika ta Kudu a ranar Talata. Rikicin ya barke ne a wuraren da ya hada da Witbank, Mpumanlaga Province, dake kasar Afrika ta Kudu din kamar yadda ‘yan Nijeriya suka tabbatar. Kakakin kungiyar ‘yan Nijeriya mazauna kasar Afrika ta Kudu, Odefa Ikele, ya shaidawa manema labarai ta wayar tarho daga Witbank cewa an kai wa bakin hari ne da safiyar ranar Talata. Harin na Talata ne ya zo ne a daidai lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari da shugaba Cyril Ramaphosa ke kokarin ganin an magance matsalolin kai wa baki hari a kasar na dindindin.