Aƙalla mutane bakwai ne aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon abinci mai guba a ƙauyen Danbaza da ke Ƙaramar Hukumar Maradun ta Jihar Zamfara.
DAILY POST ta lura da cewa lamarin ya faru ne bayan ƴan gida sun ci abincin bayan gauraya kayan lambu da masara, wanda aka fi sani da Dambu, wanda aka shirya a matsayin abincin dare.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Legas Zata hana Sana’ar Acaɓa a wasu Ƙarin Ƙananan Hukumomi
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa wadanda suka mutu, sun ƙunshi matan aure biyu da ‘ya’yansu biyar, sun mutu ne jim kaɗan bayan gama cin abinci.
A cewar wani dan uwa, Alhaji Muhammad Kabir, da mutane suka gama cin abincin, hudu daga cikin wadanda suka mutu nan take, yayin da uku kuma aka garzaya da su asibiti inda likitoci suka tabbatar da cewa sun mutu.
“An zargi wadanda suka mutu da amfani da guba wajen dafa abincin,” in ji shi.
Tuni dai aka yi jana’izar mutanen bakwai da suka mutu a garinsu na Danbaza, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Da aka tuntubi shugaban Ƙaramar Hukumar Maradun, Umar Mu’azu, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an aika wakilai daga karamar hukumar domin jajantawa iyalan mamatan.
Ƙaramar Hukumar ta buƙaci ƴan uwa da su karɓi wannan rashi a matsayin ƙaddarar Allah tare da addu’ar Allah ya baiwa iyalan hakurin jure rashi.