Dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Thiago Silva, ya bayyana mafi kyawun tunaninsa a kungiyar.
Dan wasa Silva ya koma Chelsea ne a shekarar 2020 bayan ya bar Paris Saint-Germain. Kamar yadda jaridar Daily Post ta ruwaito.
KU KARANTA: Buhari Ya Halarci Taron APC a Imo
Dan wasan na Brazil ya bayyana cewa lokacin da ya fi tunawa da shi a matsayinsa na dan wasan Chelsea shi ne ya dauke kofinsa na farko a gasar cin kofin zakarun Turai na UEFA.
Dan wasan mai shekaru 38 ya taimakawa kulob din na yammacin London ya dauki kofuna uku kawo yanzu.
Da yake magana da PariMatch, mai tsaron bayan ya bayyana cewa babban abin tunawa a Chelsea shine lashe gasar zakarun Turai ta UEFA a 2021.
Silva ya ce: “Mafi kyawun lokacin da nake sanye da rigar Chelsea tabbas shine lashe kofin Turai.
Lokaci ne na mai dimbin tarihi a rayuwata.
Bayan shekaru takwas tare da Paris Saint-Germain suna neman damar, sannan a farkon shekarar zaman sa a kungiyar kuma ya sami nasarar lashe kofin.
A wani labarin kuma: Karancin Kudi: Masu Zanga-Zanga Sun Toshe Hanyar Legas zuwa Abeokuta
Masu zanga-zangar a ranar Talata sun rufe hanyar Legas zuwa Abeokuta da titin Sango-Ota saboda gazawar su na cire kudi daga na’urar cire kudi wato ATM. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Sun yi ta kona tayoyin da ba a amfani da su a bangarorin biyu na babbar hanyar da ta haifar da cunkoson ababen hawa.