Darakta-Janar na majalisar kula da fasaha da al’adu ta kasa (NCAC), Otunba Olusegun Runsewe, ya ce yada labaran karya game da Najeriya zai hana masu zuba jari da sauran damammaki masu ma’ana ga kasar.
Da yake jawabi a karshen mako a Abuja a bikin EXPO 2022 na kasa da kasa na INAC karo na 15, ya ce ‘yan Najeriya da su kare martabar Najeriya domin ta samu ci gaba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Bom Ya Tarwatsa Diyar Na Hannun Damar Putin, Alexander Dugin
Ya lura cewa idan Najeriya ta kasance mai girma, dole ne ta tsallake kalubale.
Ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su rika hakuri da juna.
A cewarsa, yana da muhimmanci a gabatar da amfani da diflomasiyyar al’adu wajen daidaita al’amura a kasar.
Sannan ya ce “ta fannin al’adu za a iya rage rashin aikin yi da rashin tsaro.”
Runsewe ya ce taron wata dama ce ta nuna karfin kasar.
A nata bangaren, shugabar kungiyar mata ta kasa (NCWS), Lami Adamu Lau, ta yi kira ga matasa da su yi amfani da damar taron EXPO domin su samu sana’o’i da kuma dogaro da kai, domin kada ‘yan siyasa su yi amfani da su a matsayin ‘yan daba a lokacin zaben.
A wani labarin kuma Daraktoci 137 Sun Fadi Jarabawar Zama Shugabannin Makarantu
Akalla mutane 137 ne daga cikin ma’aikatan gwamnati 344 da aka nada a matsayin shugabanin makarantun hadin kan kasa 110 da ke fadin kasar nan, suka fadi jarabawar da ma’aikatar ilimi ta tarayya ta shirya, kamar yadda PUNCH ta tattaro.
Wakilinmu ya samu labarin cewa daraktoci 207 da suka ci jarabawar sanin makamar aiki ta kwamfuta, an shirya za su yi tattaunawa ta baki da baki.