Abinda Ya Kamata Ku Sani Kan Wani Ɓoyayyen Sirrin Dangantakar Tinubu Da Mutanen Arewa
Ranar Asabar a fadar Shehun Borno, Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum ya faɗi batutuwa a taƙaice amma kuma masu girma. Ya gabatar da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ga mai martaba. Zulum ya faɗa cewa Tinubu ya kasance a birnin Maiduguri musamman domin Jihar Borno da al’ummarta a lokuta na tsanani matuƙa a tarihinta na shekaru 1,200. Yayin da ya zamto cewa mafi yawan mutane sun sallamar da birnin Maiduguri saboda su tseratar da rayuwarsu daga ta’addancin Boko Haram, amma Asiwaju ya kasance a Jihar ba sau ɗaya ba.
“A lokutanmu na tsanani, Asiwaju ya na tare da mu a kowane lokaci. Ya ziyarce mu kusan sau bakwai zuwa takwas cikin shekaru bakwai baya. Babu wani mutum da ya yi mana haka”. Cewar Gwamna Zulum.
KARANTA WANNAN LABARIN: Koriya Ta Arewa Na Fama Da Karancin Abinci — Masana
Jawaban da Gwamna Zulum ya yi sun bayyana kykkyawar dangantakar zumunci da Asiwaju ya gina da Arewacin Najeriya da al’ummarta tsawon shekaru. Alaƙakar ba wai ta yau ba ce, daɗaɗɗiyar alaƙa ce da ta haifar da zumunci da jajantawa juna gami da zaman tare. Abin mamaki Tinubu ya samu karɓuwa a wajen hatta mutanen yankin Niger. Hakan ya bayyana a lokacin da jirgin yaƙin neman zaɓensa ya karɓi manyan Jihohin Arewa; Kaduna (hedikwatar Arewa), Kano (cibiyar kasuwanci) har zuwa Jihohin Daular sarakunan Fulani da Kanuri, (Sokoto da Borno).
Alamar da wani ya nuna cikin hotunan ɗumbin jama’ar da su ka fito tarbensa, ƴan Twitter sun yi iƙirarin cewa: “Ƴan Arewa ka da su damu da wannan batu na Tinubu”. Haka ne a ƙasar da siyasarmu ke ƙarfafa bambance-bambancen mu ya zama abin mamaki. Amma dai turba ce ta Arewa ta yabawa da girmama shekarun alaƙa da gwagwarmayar zaman tare”.
Da wannan dalilin yasa aka mance da ƙoƙarin ɗan takarar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da tsare-tsarensa na sanya addini da ƙabilanci da yanki wanda mutane da dama sun ƙi yarda su bi wannan turba tasa ta son kai. Tambayar da mutane ke yi ita ce mai wannan ɗan takara ya yi wa al’ummar Arewan domin ya girba ranar zaɓe ? Mutane wayayyu ne, sun san wanda ya ke tare da su a kowane lokaci akan wanda zai je gare su ya dinga iƙirarin shi nasu ne.
Tarihin alaƙar Tinubu da Arewa daɗaɗɗen abu ne. Zan yi ƙoƙarin hakaito ɗan wani abu. Tafiyar siyasar Tinubu ta fara ne a Arewa. A jamhuriya ta uku, Tinubu ya haɗa kai da marigayi Shehu Musa Ƴar’Adu’a inda ya zaɓi ya yi aiki da shi.
Tarihin alaƙar Asiwaju da Arewa abu ne daɗaɗɗe. Zan yi ƙoƙarin hakaito ɗan wani abu daga ciki. Tunda farko ma dai tarihin siyasar Tinubu ya faro ne daga Arewa. Farkon jamhuriya ta uku Tinubu ya yi mubayi’a ga marigayi Shehu Musa Ƴar’adu’a. Ya zaɓi ya yi aiki da shi duk da cewar a lokacin akwai ɗan uwansa na jini Lateef Jakande ya na takara. Lokacin da MKO Abiola ya samu nasarar zama ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar SDP, Tinubu ne ya taka gagarumar rawar ɗora Ambasa Babagana Kingibe a matsayin ɗan takarar mataimaki.
A lokuta da dama baya-bayan nan, Tinubu ya zama tamkar Kendir da ke ƙona kansa ya na haska wasu. Ya marawa burin ƴan Arewa baya kan takararsu ta shugabancin ƙasa. Misali ya goyi bayan Atiku a 2007, Nuhu Ribaɗo a 2011, shugaba Buhari a 2015 da 2019. Duk wannan ƙari ne akan irin ɗumbin mutanen da ya taimaka a Arewa su ka samu nasarar hawa gami da riƙe muƙamai daban-daban ba-zata.
Hatta Atiku da jagoran yaƙin neman zaɓensa, Gwamnan Jihar Sokoto, Tambuwal, su na cikin waɗanda su ka lashi romon tasirin siyasar Tinubu inda har ya samu nasarar zama shugaban majalissar wakilai ta tarayya a Shekarar 2011.
Baya da batun siyasa, Tinubu a kowane lokaci cikin annashuwa ya ke da Arewa. Ya na yin fiye da abin da ya ce zai yi. A matsayinsa na ɗan Najeriya da ke zaune a Najeriya a kowane lokaci a ankare ya ke da abubuwan da ke faruwa a faɗin ƙasar. Ya na faɗaɗa hannunsa ya kai ɗauki da agaji duk inda ake buƙata.
Ya ziyarci yankunan Birnin Gwari zuwa Zamfara domin samar da sulhu da ƴan bindiga gami da rarrashin al’umma da ƙarfafa musu gwiwa. Ba wani wanda ya yi wannan abu da ya yi hatta wanda ya ke iƙirarin cewa shi naku ne bai yi ba.
Tun gabatowar makonnin zaɓe ƴan adawa ke yaɗa ƙarya da furofaganda su na jefawa domin ɓata Tinubu. Mutumin da ya kawo ƙarshen tarzomar OPC, ya samarwa ƴan Arewa daraja a Legas, ana tuhumarsa da akasin hakan.
Mutumin da ya je Arewa House a Jihar Kaduna cikin watan Oktoba, ya gabatar da jawaban manufofinsa a gaban dattawan Arewa waɗanda akasarinsu mabiya Atiku ne, su ne kuma ke yaɗa ƙaryar cewa wai bai tanadarwa Arewa komai ba. Su na ta yaɗa wannan ƙarya.
Ƴan Arewa da ke zaune a Legas sun yi bayanin yadda Tinubu da tsare-tsarensa su ka ba su damar samun gidaje da kykkyawar rayuwa. Yau a Jihar Legas akwai ɗan Jihar Katsina da ke riƙe da matsayin kwamishina. Wannan al’adar ta fara tun zamanin Tinubu, kuma akwai mutane da dama ƴan Arewa da aka zaɓe su a muƙamai daban-daban. Akwai kuma miliyoyin ƴaƴan ƴan Arewa da su ka amfana da shirin ilimi kyauta wanda gwamnatin Tinubu ta samar ba tare da nuna bambanci ba.
Tunda farko su na yaɗa farfagandar cewa wai Tinubu ba shi da lafiya, ba ya iya tsayuwa a wajen yaƙin neman zaɓe. Duk wannan ƙarerayi ne, kuma yanzu ne jama’ar Najeriya za su zaɓi ɗan takarar da su ka aminta wanda ya ke da ƙwaƙwalwa da tunanin samar da cigaba ya kuma yi aka gani.
Zaratan magoya bayan Asiwaju za su fito a ranar wannan Asabar, su kawar da bambancin batun ƙabila da yanki, su zaɓi hanyar tsira wacce ke cike da gaskiya da adalci wacce za su ga kykkyawan sakamako a cikinta.
A matsayin jami’in mulkin mallaka, Mista Brian Sharwood Smith ya rubuta bayanai kan dangantakar ƙasar Birtaniya da Arewacin Najeriya kan mulkin mallakar da aka yi wa Najeriya, Tinubu ya zo daga Legas ya na magana ba Hausa ko Filatanci amma a kowane lokaci ya kasance aminin Arewa. Mutane masu gaskiya da amana ƴan Arewa sun shirya tabbatar da abota da soyayyar Tinubu a gare su.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Abdulaziz Abdulaziz
Mataimaki na musamman ga Tinubu kan harkokin sadarwa da hulɗa da al’umma ya fitar.