Abiodun Ya Kori Ɗan Kwangila, Ya Ba FG Makonni Biyu Ta Gyara Titin Legas-Abeokuta.
Gwamna Dapo Abiodun na Jihar Ogun ya baiwa Gwamnatin Tarayya wa’adin makonni biyu da ta gyara babbar hanyar Legas-Ota-Abeokuta data lalace.
Ya sha alwashin karbar ragamar aikin sake gina hanyar idan Gwamnatin Tarayya ta gaza gyara shi a cikin wannan lokacin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zaben 2023: Jihar Kano Nada Yan Takarar Gwamna Daga Jam’iyyu 14 – INEC
Abiodun ya bayyana hakan ne jim kaɗan bayan ya duba wasu munanan ramukan hanyar mai tsawon kilomita 52.5 a yankin Ewekoro, ranar Asabar.
A cewarsa, matakin ya zama wajibi ne bayan Gwamnatin jihar tare da jihar Legas sun yi ƙoƙarin jawo hankalin Gwamnatin Tarayya a lokuta da dama, ta hannun ofishin ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, kan rashin kyawun yanayin hanyar ba tare da wani amsa mai kyau ba.
Gwamnan wanda ya nuna damuwarsa kan wahalar da masu ababen hawa ke fuskanta a kan hanyar, ya bayyana cewa Gwamnatinsa ba za ta naɗe hannunta ba, ta bar ƴan Jahar su ci gaba da shan wahala saboda sakacin hukumar da ke kula da wannan hanya.
“Idan bayan makonni biyu, Gwamnatin Tarayya ta ki fara aiki a wannan hanyar, zan karɓe ta in sake gina ta,” in ji shi.
A yayin da yake kira ga al’ummar jihar musamman waɗanda ke zaune a kan titin da su yi hakuri, Gwamnan ya bayyana cewa dalilin da ya sa ya kai ziyarar ne domin duba irin ci gaban da aka samu a yankunan da ake fama da matsalar ababen more rayuwa a gundumomin Ogun ta Tsakiya da kuma Ogun ta Yamma da nufin tabbatar da hakan.
matakin barnar da aka yi wa wasu manyan tituna a yankunan domin fitar da mafi kyawun hanyar sake gina su.
Ya lura cewa hanyar da aka baiwa Julius Berger kimanin shekaru 15 da suka wuce an yi watsi da ita wanda ya sa ba za a iya binta ba.
Ya ce duk da ayyukan da ake yi a kan titin, wasu daga cikin kamfanonin blue chip da ke gefen titin sun kasa tallafawa ƙoƙarin Gwamnati ta hanyar Corporate Social Responsibility (CSR).
Abiodun ya soke kwangilar da ya baiwa Kamfanin gine-gine na RAJCOM, na sake gina hanyar Iwoye-Owode a karamar hukumar Yewa ta Kudu bisa karancin kayan aiki
Gwamnan wanda ya sanar da dakatar da kwangilar a lokacin da yake duba hanyar mai tsawon Kilomita 25.4, ya nuna rashin gamsuwar sa.