Gwamna Nasir El-Rufai ya ce ‘yan adawar jam’iyyar, APC, da dan takararta na shugaban kasa, Bola Tinubu na da makudan kudade a hannun su gabanin babban zabe.
A ranar Alhamis din da ta gabata ne gwamnan ya yi jawabi ga al’ummar jihar Kaduna sakamakon karancin sabbin takardun kudi na naira bayan da babban bankin Najeriya CBN ya sake fasalin naira 200 da N500 da kuma N1000.
KU KARANTA: Wike ya koma APC a hukumance
El-Rufai ya ce CBN da sauran jami’an gwamnatin tarayya da suka “ji dadi” sun gamsar da shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa yana da kyau a kwato kudin talakawan da wasu suka yi sama da fadi dasu.
Gwamnan ya koka kan yadda ake hana kanana da matsakaitan ‘yan kasuwa samun jarin su, wanda hakan ke kawo tsaikon ciniki da musayar kudi a tsakanin su.
El-Rufai ya tabbatar da cewa kokarin ganin gwamnatin Buhari ta yi gyara wajen aiwatar da manufofin da yake fatan cimma, basu yi nasara sakamakon yadda suka sanya mutane cikin hali na kunci.
A dai yayin hirar ne kuma Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya bukaci mazauna jihar da su ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kudin Naira.
Umarnin nasa na zuwa ne bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa duka tsofaffin takardun Naira 1,000 da kuma N5,000 sun saɓawa doka, a don haka bankuna baza su kara karbar kudin ba.
A wani labarin kuma: Lokacin da kuka faɗa na daina karɓar kudi ya saɓawa doka – El-rufai ya gargadi Buhari kan tsohon kudi
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, a ranar Alhamis, ya bukaci mazauna jihar da su ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kudin Naira.
Umurnin nasa na zuwa ne bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana a kafar yada labarai ta kasa da safiyar yau cewa duka tsofaffin takardun Naira 1,000 da kuma N5,000 sun saɓawa doka.