By Ishaq Dabai
Abokan cinikin gidan waya na Najeriya (NIPOST) dake jihar Bauchi sun yi kira da a gudanar da gangamin wayar da kan jama’a game da ayyukan hukumar a jihar.
Sun yi wannan kiran ne a Bauchi ranar Asabar a wani taron abokan cinikayya da aka shirya don tunawa da “Ranar Post ta Duniya” da ake yi kowace shekara a ranar 9 ga watan Oktoba.
Daya daga cikin kwastomomin su Mista Sulaiman Hamisu, yace akwai bukatar NIPOST ta fara kamfen na fadakar da ayyukanta a jihar.“Mutane basu san ayyukan NIPOST ba, sun san gidan waya amma basu san ayyukan da ake yi da kuma ingancin ayyukan nasu ba.
Don haka ya kamata NIPOST ta kara gangamin wayar da jama’a don samar da fadakarwa da kuma nuna ayyukanta ga ‘yan kasa,” in ji shi.
Duk da haka wani mai suna Nura daya daga cikin a bokan cinikayyar su, ya yaba wa NIPOST saboda samar da ayyuka masu inganci da arha ga hukumomin da yawa inda ya kara da cewa isar da hidimar hukumar tayi kyau.
Ita ma Wata a bokiyar cinikinsu mai suna Misis Zainab Abdullahi, tace da yawa daga cikin al’ummomin basu san ayyukan NIPOST ba, ya kara da cewa mafi yawan yaran makaranta kasa da shekaru 18 basu da masaniya sosai kan ayyukan hukumar.
A nata bangaren, Misis Jedidah Sambo, Manajan Shiyyar NIPOST, ta jihar Bauchi tace hukumar ta kara yawan kudin da take caza na aikawa da sakonni don samar da ingantaccen ayyukan a cikin kasar. A yanzu kudin gidan waya ya koma daga N50 zuwa N250.