Biyo bayan kin bayyana sunan dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Chelsea dake kasar Ingila Tammy Abraham cikin jerin sunayen da za su wakilci Nijeriya, mai horas da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa kasar Ingila Gareth Southgate ya sanya sunan dan wasan cikin ‘yan wasan da za su wakilci kasar ta Ingila a wasannin da za ta fafata a kwanan nan.
Tammy Abraham dai yana da damar ya zabi kasar kasar da zai bugawa wasa tsakanin Nijeriya da Ingila, sai da mai horas da ‘yan wasan Nijeriya Gernot Rohr ya ce a yanzu haka Nijeriya ba ta bukatar dan wasan.
Dan wasan mai shekara 22 yanzu haka ya zurawa kungiyar kwallon kafa ta Chelsea kwallaye 7 a wasanni 7 da ya buga a gasar Firimiyar kasar Ingila a kakar wasanni ta bana.
Nijeriya dai tana fama da matsalar ‘yan wasan gaba biyo bayan ritaya da Odion Ighalo ya yi.