Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello yayi ikirarin cewar abubuwan ci gaba daya kawo jihar Kogi a yanzu ba komai bane a kan ayyukan alkairin da zai kuma malalawa idan ya kuma samun damar danewa bisa kujerar mulki idan aka kuma zaben sa.
Gwamna Yahya Bello ya bayyana haka ne a babban birnin jihar Kogi, Lokoja a lokacin da suke wani zama da masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar APC reshen jihar Kogi da wasu Gwamnoni masu ci a yanzu guda biyu a kasar nan don tattauna rikita rikitar zaben fittar da gwanin dan takarar da Gwamnan jihar a karkashin inuwar Jam’iyyar APC mai mulki.
Daga cikin Gwamnonin da suka halarci zaman sun hadar da Gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu da Gwamnan jihar Yobe Mala Buni da kuma tsohon Gwamnan jihar Bauchi MA.
Gwamnonin sun yabawa Jihar Kogin bisa yadda suka zage dantse a lokacin zabukan 2019 don ganin Buhari ya lashe zabe inda suka bukace su da su kuma zage damtse ganin APC ta kuma lashe zabe.
Yahaya Bello ya cika bakin cewar lokacin daya karbi jihar Kogi, jihar na fama da kalubalen tsaro ciki harda ayyukan taaddanci da kuma sace sacen mutane amma yanzu batun ya zama tarihi a karkashin Gwamnatin sa.
Yanzu haka dai shirye shirye sun yi nisa kan zaben Gwamnan jihar Kogi da zai gudana a ranar 16 ga watan Nuwambar wannan shekarar da muke a ciki.