Daga wakilin Dimukaradiyya Mukhtar Yakubu Kano.
Fitacciyar Mawakiya kuma Sha’ira. A fagen yabon Manzon Allah S A W. Hajiya Maryam Saleh Fantimoti. Ta bayyana harkar yabon Manzon Allah S A W da cewar harkar yabo baiwa ce da kuma basira, sabanin yanzu da aka mayar da abin a matsayin sha’awa musamman a bangaren mata.
Fantimoti ta bayyana hakan ne a lokacin tattaunawar su da wakilin Dimukaradiyya dangane da yadda a ke gudanar da harkokin a wannan lokacin.
Inda ta ke cewa ” A yanzu an mayar da abin na sha’awa, sai ka ga wata idan ta kalli Mawakiya a kan Mumbari, sai sha’awa ta fisgota ta shigo, sabanin a baya da muke yi, wadda sai mutum Yana da baiwar wakar ba wani muka kalla yana yi ba. Allah ne ya ba mu baiwar a jikin mu take.”
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan sanda sun Kama wasu Mutane da ake Zargin Yan Kungiyar Asiri ne
Ta ci gaba da cewar, “Akwai matakai da yawa da a ke bi a wajen wakokin yabon Manzon Allah S A W, amma Sam ba a bin su sai a rinka yin wani abu daban da sunan yabo. Don haka abubuwan da su ke cikin Halarar yabo a yanzu wallahi ba sa cikin harkar fim ta nanaye. Domin ni Maryam Fantimoti ina cikin Halarar yabo kuka ina cikin Nanaye, amma ina tabbatar maka abin da ya ke cikin Halarar yabo ba ya cikin harkar fim ta nanaye.
Saboda a nanaye babu yadda za a yi ka dauki wakar mutum ka je kana yi ba tare da ya daure ka ba, Amma mu sai ka je wajen taro kawai sai ka ji an dora wakar ka wani yana yi, kana yin magana, sai a ce a a, ai Annabi ne, don haka abubuwa da yawa suna faruwa da ba za su fadu ba Amma sai a rinka fakewa da Annabi. ”
Daga karshe ta yi kira ga masu harkokin yabon Manzon Allah S A W, da su ji tsoron Allah su sani cewar ba a yin wasa da soyayyar Manzon Allah S A W.
Comments 1