Sufeto Janar na ‘yan sandan Nijeriya, Mohammed Adamu, ya ce birnin tarayya Abuja yana daya daga cikin biranen duniya da ke da karancin aikata laifuka.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, DCP Frank Mba shi ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a birnin tarayya Abuja. Adamu ya ce zancen cewa birnin tarayya Abuja yana daya daga cikin biranen da ake zaune lafiya babu wani tantama duba da rahotanni aikata laifuka na manyan birane a duniya.
Ya kara jaddada cewa; birnin tarayya Abuja ana zaune lafiya, kuma birnin ne da ba ya cikin wani barazanar rashin tsaro kamar yadda aka yadawa a kafafen sada zumunta.
Sufeton ‘yan sandan ya ce; kamar sauran wurare a duniya, haka ma kasarnan ke fama da matsalar tsaro. Adamu ya nemi ‘yan kasa masu bin doka da oda da su ci gaba da harkokinsu ba tare da wani firgici ba.