Kwamishinan ilimi na jihar Kano, Dr Muhammad Sunusi Sa’idu Kiru, ya danganta jinkirin fitar da sakamakon jarabawar jihar da yawan mabukata jarabawar.
Kiru ya bayyana hakan ne a yayin wani taron tattaunawa na kwana daya kan harkokin ilimi da kalubalen tsaro a Najeriya, wanda kungiyar PERL-ECP ta shirya a Kano.
Jaridar Dimukuradiyya ta rawaito Kiru yana cewa Sashen kula da albarkatun Ilimi na Kano (KERD) ya cika da tsare-tsare da gudanar da jarrabawar kammala makarantun furamare ta kwamen intares da jarabawar kwalafayin don tantancewa domin gudun tauye babban aikinta na bunkasa tsarin.
Kwamishinan ya kara da cewa tun daga nan ya rubutawa gwamnatin jihar Kano wasikar neman a kafa hukumar jarabawar jihar Kano domin gudanar da dukkan jarrabawar cikin gida.
Kafa sashin ilimin yara mata
Kiru ya kuma ce gwamnati ta kafa sashen koyar da yara mata domin kula da yaran ta fuskar ilimi, don haka nema gwamnatin Kano ta himmatu wajen samar da ilimi kyauta kuma dole ta hanyar samar da karin makarantu, da kayayyakin koyo, biyan kudaden jarrabawa da dai sauransu.
Kwamishinan ya bayyana cewa gwamnatin jihar Kano ta kafa karin makarantun sakandare na mata guda biyu a cikin babban birnin jihar. Yana mai cewa za a kafa makarantun mata sama da 100 a cikin kananan hukumomi 44.
Kwamishinan ya yi nuni da cewa gwamnatin jihar ta dauki kwararan matakan tsaro domin kare rayukan dalibai da suka hada da rufe makarantun kwana da mayar da wasu makarantun jeka ka dawo.
“Gwamnati ta biya Kashi 100% na kudaden jarrabawa ga ‘yan mata, kuma ta samar da karin makarantun kwana na ‘yan mata tare da isassun kayayyakin koyo da kayayyakin more rayuwa don kula da lafiyarsu,” in ji Kiru.