Kungiyar kwallon kafa ta AC Milan dake ƙasar Italiya ta sayi dan wasan gaba na Chelsea Olivier Giroud kan kuɗi Euro miliyan biyu.
Olivier Giroud ya gamu da cikas a Ƙungiyar ta Chelsea tun bayan da ya tsohon kocin Chelsea Antonio Conte.
Dan wasan dan kasar Faransa ya haɗe da Chelsea ne a shekara ta 2018 daga kasar bayan da wa’adin Kwantiraginsa ya kare da ita.
Ya ci kwallaye 39 wa Chelsea a wasanni 119 da ya buga mata, kazalika ya samu nasarar lashe kofunan zakarun turai ta Champions League da Europa sai kuma kofin FA.
A yanzu haka zai sanya riga mai lamba 9 ne wa AC Milan abinda ake ganin zai taimaka masa wajen maido masa da karsashinsa.