An samu karin ‘yan Nijeriya kusan 239 ne aka tabbatar a ranar Asabar sun sake kamuwa da cutar korona, adadin masu cutar yanzu ya kai 4,151, in ji Hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta Nijeriya, NCDC.
A sakon Twitter da ta fitar daren Asabar, hukumar NCDC ta ce mutum 66 sun warke a cikin sa’a 24 da ta wuce, yanzu duka-duka wadanda suka warke daga annobar 745 a fadin kasar.
Jihar Legas, an sake gano mutum 97 da korona ta shafa, jihar ce annobar ta fi kamari kuma ta fara bulla , alkaluman NCDC sun ce yanzu jihar na da yawan masu korona 1,764.
Haka zalika, an ba da rahoton mutum goma sha daya sun sake mutuwa a cikin sa’a 24, abin da ya sa yawan mutanen da suka mutu sakamakon korona ya kai 128.
Jihar Kano wadda ta fi yawan masu cutar a arewacin Nijeriya, an sake gano mutum 29 a ranar Asabar da suka kamu, yanzu adadin masu korona a jihar ya kai 576.
Jihar Bauchi a wannan karon ita ce tazo ta biyu a yawan wadanda suka kamu a ranar Asabar inda mutum 44 suka sake kamuwa abin da ya kai adadin masu cutar a jihar yanzu 161.
Jihar Katsina ta sake samun mutum 19 da suka sake kamuwa da cutar, sai Abuja, babban birnin tarayyar Najeriyar an sake samun mutum 7 da suka kamu da cutar, sai Borno 17, Kawara 6, da kuma Oyo 5.
Sauran jihohin da ake sake samun wadanda suka kamu sun hadar da Kaduna 3, Sokoto 3, Adamawa 2, Kebbi 2 , Plateau 2, Ogun 2 da kuma Ekiti mai 1.