Hukumar yaki da dakile yaduwar cututtuka ta Nijeriya, NCDC ta ce karin mutane 216 sun kamu da cutar Korona a kasar.
Legas ke da adadi mafi yawa na karin masu cutar ta Korona da aka samu da adadin mutane 74, sai Katsina 33, Oyo 19, Kano 17, Edo 13, Zamfara 10, Ogun, Borno da Gombe dukkaninsu ke da mutane 8-8.
Sauran jihohin sun hada da Bauchi da Kwara masu mutane 7-7, Abuja 4, Kaduna da Inugu 3-3, sai jihar Ribas da ta samu karin mutane 2.
Zuwa yanzu jumillar yawan mutanen da suka kamu da cutar Korona a Nijeriya ya kai dubu shida da 175, daga cikinsu kuma dubu 1 da 644 sun warke, yayinda 191 suka mutu.
Rahoton da hukumar ta NCDC ta wallafa a daren jiya litinin, ya nuna cewar an samu sabbin kamuwar ne a jihohin Nijeriya 15.
Har yanzu Legas ke sahun gaba wajen yawan wadanda cutar ta Korona ta kama da adadin dubu 2 da 550, daga cikinsu kuma 556 sun warke, yayin da 36 suka mutu, sai kuma Kano mai yawan mutane 825, daga ciki 111 sun warke, yayin da 36 suka mutu.