By Abbas Yakubu Yaura
An tabbatar da mutuwar mutane 52 a cikin sa’o’i 72 sakamakon hare-haren ‘yan bindiga a fadin jihar Sokoto.
A baya Gwamna Aminu Tambuwal ya tabbatar da mutuwar mutane 15 zuwa 12 a karamar hukumar Ilella da uku a karamar hukumar Goronyo.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa a yayin da gwamnan ya ziyarci wuraren a ranar Laraba, adadin ya kai mutane 43.Kauyukan da aka kai harin sun hada da Kalmalo, Munwadata, Sarma, Runji, Tunbulunkun, Tafkin Taramniya da Masasa.
Sai dai baya ga mutane 43 da aka kashe kamar yadda Tambuwal ya tabbatar, rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto a ranar Alhamis tace an kai hari a kauyuka uku na karamar hukumar Sabon Birni, inda aka kashe mutane tara.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Abubakar Sanusi, ya shaida wa wakilinmu ranar Alhamis cewa an kashe mutane tara a wasu hare-haren da aka kai tsakanin ranakun 15, 16, da 17 ga watan Nuwamba, 2021.
Kazalika ASP Sanusi yace, “Harin farko da aka kai a Garin Zago a karamar hukumar Sabon Birni ya yi sanadin mutuwar mutane uku yayin da wasu kuma aka yi garkuwa dasu.
“A ranar 16 ga Nuwamba, 2021, an kai wa wata mota hari a kauyen Gaji amma ba a samu asarar rai ba.”Harin na uku ya faru ne a ranar 17 ga watan Nuwamba, 2021 a kauyen Sangirawa inda maharan suka kashe mutum shida.”