Hukumar kula da cututtuka masu yaduwa ta Kasa NCDC ta ce adadin wadanda suka mutu sakamakon cutar mashako a fadin kasar ya kai 34, yayin da jihar Kano ta ke da mutane 100 ake zargin sun kamu da cutar.
Hukumar NCDC, ta shafinta na yanar gizo a ranar Lahadi, ta ce an samu mace-mace tsakanin Disambar 2022 zuwa farkon Janairun 2023; daga Legas, Kano, Yobe da Osun, kuma sun ba da rahoton bullar cutar, inda jihar Kano kadai ta ke mutane 25 da suka mutu.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Hukumar ta kuma dora alhakin karuwar kamuwa da cutar da sake bullowa a kan karancin allurar rigakafin da ake yi a fadin kasar.
KU KARANTA KUMA Gwamnatin Kano Ta Tabbatar Da Bullar Cutar Mashako 24 Sun Mutu
Mashako cuta ce mai rigakafin wacce ta zama ruwan dare shekaru da yawa da suka gabata.
Saboda tasirin shirye-shiryen rigakafin yara, yawancin mutane sun manta yadda ake kamuwa da mashako.
“Gaskiya ne cewa mun sake samun dowowar cutar mashako a yanzu yana nuna cewa an sami raguwa sosai wajen amfani da allurar rigakafi a tsakanin al’ummarmu.
“Wannan rage yawan rigakafi na jama’a ya haifar da lamuran da muke gani.
“Ba batun mashako ke yaduwa daga jiha zuwa jiha ba, kwayoyin cutar da ke haddasa cutar suna nan a ko’ina a cikin muhallinmu.
“Duk jihar da kuka sami mashako a yanzu, za ku iya gano cewa za a danganta ta da ɗaukar allurar rigakafi, ko dai a gaba ɗaya ko a cikin jama’a,” in ji shi.
A halin da ake ciki, an gano masu cutar mashako a Kano daga 25 zuwa 100 cikin kasa da makonni biyu.
Mutane uku ne suka mutu a kananan hukumomi 13 na jihar.
A Wani Labarin Kuma Ganduje Ya Kaddamar Da Taken Jihar Kano
Gwamnan jihar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar da taken jihar Kano, wanda za a rika yin sa a yayin kowanne taro bayan an yi take Nigeria.
Da yake jawabi gabanin kaddamar da taken Gwamna Ganduje yace an samar da taken ne don sanar da al’umma musamman yara yan makarantar muhimmancin jihar da kuma tarihin ta.